Majalisar dattawa ta yarje da manufar sauya kwalejin Kadpoly zuwa Jami'a

Majalisar dattawa ta yarje da manufar sauya kwalejin Kadpoly zuwa Jami'a

- Majalisar dattawa ta amince da manufar da aka gabatar mata na sauya kwalejin Kaduna Polytechnic zuwa cikakkiyar Jami'a

- Ta ce abinda rage yanzu kawai shine ta gabatar da kudurin ga majalisar dokoki domin ta sanya hannu kafin ta mika kudurin ga shugaba Buhari

Majalisar dattijai ta yi zama na uku akan kudurin mayar da Kaduna Polytechnic ta koma cikakkiyar Jami'a ta jihar Kaduna, sun yankewa shawarar mayar da ita (City University of Technology).

Hakan ya biyo bayan nazarin da kwamitin karatun gaba da sakandare ta yi wato (Tertiary Education and TetFund) a turance, wadda Sanata Jibrin Barau (APC, Kano) ya jagoranci kwamitin. Kudurin wanda, Sanata Shehu Sani (PRP, Kaduna) ya kai.

Majalisar dattawa ta yarje da manufar sauya kwalejin Kadpoly zuwa Jami'a

Majalisar dattawa ta yarje da manufar sauya kwalejin Kadpoly zuwa Jami'a
Source: UGC

Bayan an gama bayar da rahoto, majalisar dattijan ta amince da kara zama na uku akan kudurin jiya Talata.

Ana sa ran majalisar dattijan za ta aika da kudurin zuwa ga dakin majalisar wakilai domin su sanya hannu kafin a gabatar da kudurin gaban shugaban kasa Muhammadu Buhari domin shima ya sanya hannu, domin mayar da kudurin doka.

KU KARANTA: Farfado da yankin arewa maso gabas shine muhimmin abun da muka sako gaba - Osinbajo

Bangaren ilimi na ta samun kalubale a Najeriya, musamman makarantun gaba da sakandare da ba wuya ma'aikatan suke tafiya yajin aiki saboda wasu bukatun su da suke ta faman kai ruwa rana da gwamnati akai.

Sai dai kuma a wannan makon ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa kungiyar ASUU makudan kudaden da suka yi yarjejeniya akai, akwai yiwuwar gwamnatin ta gama daidaitawa da kungiyar ASUU din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel