Farfado da yankin arewa maso gabas shine muhimmin abun da muka sako gaba - Osinbajo

Farfado da yankin arewa maso gabas shine muhimmin abun da muka sako gaba - Osinbajo

- Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce za su yi iya bakin kokarin su wurin ganin sun dawo da martabar yankin arewa maso gabas

- Ya ce gina yankin arewa maso gabas shine muhimmin abun da gwamnatin shugaba Buhari ta sako a gaba

A jiya Talata ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya sake jaddada kudurin gwamnatin nan na sake gina yankin arewa maso gabas, wanda ya lalace sanadiyyar rikicin Boko Haram.

"Babban kalubalen da ke gaban wannan gwamnatin ta mu shine sake gina yankin arewa maso gabas," Osinbajo ya bayyana hakanne a fadar Sarkin Borno jim kadan bayan ya kammala kaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar mai barin gado yayi.

Farfado da yankin arewa maso gabas shine muhimmin abun da muka sako gaba - Osinbajo

Farfado da yankin arewa maso gabas shine muhimmin abun da muka sako gaba - Osinbajo
Source: Facebook

Ya cigaba da cewa, "gina yankin nan yana daya daga cikin abubuwan da gwamnatin nan ta sanyo a gaba," in ji shi, ya tabbatar da cewa tare da kafa Kwamitin Farfado da Yankin Arewa maso Gabas, tare da sanya dokar a cikin dokokin kasa, zai taimaka mutuka wurin farfado da yankin.

Ya yabawa gwamnan jihar mai barin gado, Kashim Shettima da irin namijin kokarin da yayi wurin ganin ya gabatar da ayyukan da za su farfado da jihar.

KU KARANTA: Laifin gwamnati ne matsalar tsaron Najeriya - PDP

Haka shima Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Kanemi, ya roki gwamnatin tarayya ta bayar da kulawa ta musamman ga al'ummar yankin musamman ma wurin bayar da mukaman gwamnati, saboda irin kashe al'ummar yankin da 'yan ta'addar Boko Haram suka yi.

Ya yabawa gwamnatin Shettima da ta sanya sunan shi a daya daga cikin makarantu arba'in da aka bude a jihar.

Ya kuma bayyana mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin babban aboki na jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel