Yan bindiga sun hallaka yan sa kai 5 a jihar Katsina

Yan bindiga sun hallaka yan sa kai 5 a jihar Katsina

Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kisan yan banga biyar da yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari a ranar Talata, 21 ga watan Mayu.

Kakakin rundunar yan sanda, SP Gambo Isa ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar a Katsina.

Ya bayyana cewa kisan ya faru ne a kauyen Sabon-Layi dake karamar hukumar a lokacin da mambobin kungiyar bangan wanda aka fi sani da “Yan Sa kai” suka shiga jeji don fuskantar yan bindigan.

A cewar shi, yan bindigan sun kashe yan bangan ne a lokacin musayar wuta.

Yan bindiga sun hallaka yan sa kai 5 a jihar Katsina

Yan bindiga sun hallaka yan sa kai 5 a jihar Katsina
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa rundunar ta kafa hadin jami’an ta wanda DPO dake kula da yankin ya jagoranta don neman gawawwakin su, sun kuma gano sansanin yan bindiga a cikin jejin.

Kakakin rundunar yace a halin yanzu ana farautan yan bindigan.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Yan majalisar wakilai na yunkurin haramta amfani da jakar leda

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babbar jam'iyyar adawar Najeriya wato jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa rikicin da ake ta faman fuskanta a kasar nan ta fannin tsaro ya na da nasaba da yadda gwamnatin shugaba Buhari ke gabatar da mulkin ta.

Sanata Umaru Tsauri, sakataren jam'iyyar PDP na kasa shine ya bayyana hakan ga manema labarai a wata hira da yayi da su.

Ya ce rashin bayyanawa al'umma gaskiyar abinda ke faruwa a kasar nan da gwamnati take yi shine ummul aba'isin abinda ya jefa kasar cikin halin ha'ula'i na rashin tsaro.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel