Wata sabuwa: Yan majalisar wakilai na yunkurin haramta amfani da jakar leda

Wata sabuwa: Yan majalisar wakilai na yunkurin haramta amfani da jakar leda

Majalisar wakilai tayi na’am da wani rahoto kan wata doka da ke haramta amfani da jakar leda, kera ta da kuma shigo da ita don amfanin gida ko na kasuwa.

Anyi na’am ne da rahoton a ranar Talata, 21 ga watan Mayu a kwamitin majalisar karkashin jagorancin mataimakin kakaki majalisa, Yussuf Lassun (APC-Osun).

Dokar na neman a magance illar jakar leda kan teku, kogi, korama, daji, namun daji da kuma mutane a lokacin da aka gabatar dashi.

Mohammed Monguno (APC Borno) ne ya gabatar da dokar wanda majalisar dattawa ta gabatar a gaban majalisar wakilai.

Rahoton ya ba da shawarar cewa masu siyar da kayayyaki za su fara amfani da jakar takarda wajen siyar da kayayyakinsu maimakon jakar leda ko kuma su fuskanci hukunci na aikata laifi da zaran an gabatar da kudirin.

Wata sabuwa: Yan majalisar wakilai na yunkurin haramta amfani da jakar leda

Wata sabuwa: Yan majalisar wakilai na yunkurin haramta amfani da jakar leda
Source: Twitter

Ya bayyana cewa wadanda ke kera jakar leda da nufin siyarwa za su fuskanci hukunci na aikata laifi.

Rahoton ya kuma bayyana cewa duk mutumin da ya shigo da jakar leda don siyarwa ko kuma aka kama shi yana yawo da ita toh shima zai fuskanci hukuncin aikata laifi.

KU KARANTA KUMA: Tsaffin hadiman minista sun maka shi a kotu saboda kin biyansu albashi

“Duk mutumin da aka kama da laifi za a ci shi tarar N500,000 ko kuma zaman gidan kurkuku da ba zai wuce shekaru uku ba ko kuma duka biyun."

Rahoton yace duk kamfanin da aka kama da laifi za a ci ta tarar akalla naira miliyan biyar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel