Mu na daukar nakasassu aiki a kamfanin NNPC – Ughamadu

Mu na daukar nakasassu aiki a kamfanin NNPC – Ughamadu

Babban kamfanin man Najeriya NNPC ya bayyana cewa ba a cire masu fama da nakasa daga cikin wadanda za a dauka aiki ba. Kakakin kamfanin watau Ndu Ughamadu ya bayyana wannan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga shiyyar yada labarai na kamfanin NNPC, ba a ware wadanda Allah ya jarabta da wata larurar nakasa daga jeringiyar mutanen da kamfanin zai iya dauka aiki ba.

Mai magana da bakin kamfanin NNPC na kasar, Ndu Ughamadu yake cewa su kan dauki har da nakasassu aiki kamar yadda yanzu haka akwai mai nakasa da yake aiki a shiyyar yada labarai na kamfanin.

KU KARANTA: Wasu Jihohi za su tsiyace idan albashi ya karu a Najeriya

Mu na daukar nakasassu aiki a kamfanin NNPC – Ughamadu

Ughamadu yace Guragu, kurame, makafi, bebaye da kutare na iya aiki a NNPC
Source: UGC

Mista Ughamadu yayi karin haske inda yake cewa a tsarin taimakawa al'ummar garuruwan matatun man fetur yake wato Corporate Social Responsibility na kamfanin NNPC, masu nakasa da-dama su kan samu shiga musamman a yankin Neja-Delta na kasar.

Ndu Ughamadu ya bayyana wannan ne a lokacin yayi hira da manema labarai Ranar Talata 21 ga Watan Mayu a Abuja bayan wata kungiya ta koka da cewa ba a basu damar aiki a kamfanin man na NNPC.

Mista Godstime Onyegbula, shi ne shugaban wannan kungiya wanda ya jagoranci zanga-zanga domin nuna rashin jin-dadinsu na ware su da ake yi daga samun aiki saboda su na fama da larura a halittar su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel