Gwamnan Imo ya gargadi Shugaban VON Okechukwu ya daina bata masa suna

Gwamnan Imo ya gargadi Shugaban VON Okechukwu ya daina bata masa suna

Mun ji cewa gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya gargadi Darekta Janar na hukumar VON na Najeriya watau Mista Osita Okechukwu da ya daina fitowa yana sukarsa har ya ci masa mutunci.

Mai girma gwamnan yace Osita Okechukwu yana yawan yin kalaman da su ke bata sa a idanun jama’a. Gwamnan yace duk da cewa an gama rikicin yakin neman zaben 2019, har yanzu bai tsira ba.

Gwamnan jihar na Imo mai shirin barin-gado yake fadawa Osita Okechukwu cewa ba don irin kokarin da yayi ba, da har gobe babu wanda yake jin labarin jam’iyyar APC a Kudu maso Gabashin kasar.

Okorocha yana maidawa Mista Osita Okechukwu martani ne bayan ya fito yace gwamnan ne ya wargaza APC a Kudu maso gabashin kasar. Gwamnan ya kare kan sa, yana cewa su su kawo APC a yankin.

KU KARATA: Tinubu ya farka daga mafarkin zama Shugaban kasa – Matasan Arewa

Gwamnan Imo ya gargadi Shugaban VON Okechukwu ya daina bata masa suna

Okorocha ya ja-kunen Osita Okechukwu ya daina zaginsa
Source: Depositphotos

Mai girma gwamnan yayi wannan jawabi ne ta bakin babban Sakatarensa na yada labarai, Sam Onwuemeodo. Gwamnan yace shi ne ya rika yawo a Kudancin kasar domin APC ta samu karbuwa a 2015.

Haka zalika, gwamnan ta bakin Onwuemeodo yace a dalilin kokarin da yayi ne jam’iyyar APC ta samu kujeru 24 a majalisar dokoki da kuma ‘yan majalisar tarayya 5 da Sanata 1 a zaben baya na 2015.

Rochas Okorocha yace a zaben 2019 ne APC ta dauko mutane irinsu Osita Okechukwu, wanda su kayi ta kokarin ganin bayan gwamnan, kuma a karshe hakan yayi wa APC nakasa ta sha kashi a zaben

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel