Hadari ba sai a mota ba: Kasa ta halaka kananan yara 3 a Kano, 3 sun tsallake rijiya da baya

Hadari ba sai a mota ba: Kasa ta halaka kananan yara 3 a Kano, 3 sun tsallake rijiya da baya

Jami’an hukumar kwana kwana ta jahar Kano sun samu nasarar ceto wasu kananan yara guda uku da kasa ta ruguzo ta dannesu a kauyen Kuka dake cikin karamar hukumar Gezawa ta jahar Kano, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin hukumar, Alhaji Saidu Muhammad ne ya bayyana haka a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, inda yace a ranar Litinin hadarin ya faru, sai dai yace baya ga yara 3 da suka ceto, akwai wasu guda uku da suka gamu da ajalinsu a karkashin kasar.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Dakarun Soji sun tattara mazauna wani kauye sun canza musu wajen zama

“Da misalin karfe 11:59 na safe me wani mutumi mai suna Malam Mukhtar ya kiramu ta wayar tarho ya shaida mana cewa kasa tarin kasa ta danne wasu yara shida yayin da suke hakar kasar a kauyen Kuka.

“Ba muyi wata wata ba muka aika da jami’anmu zuwa inda lamarin ya auku, isarmu keda wuya muka zakulo yaran muka dangana dasu zuwa ga Asibiti, inda a can ne bayan likitoci sun dubasu suka tabbatar da mutuwar guda uku daga cikinsu.” Inji shi.

Saidu ya bayyana sunayen yaran kamar haka Abdullahi Abdul mai shekaru 12, Aminu Isa 13, Bashir Umar 13, Nazir Rabiu 17, Usman Garba 14, da kuma Zakari Dandolo mai shekau 12, ya kara da cewa sauran ukun da suka rayu kuma suna dauke da karaya a jikinsu.

Daga karshe Saidu yace sun mika gawarwakin wadanda suka mutu, da kuma wadanda suka jikkata ga dakacin kauyen Gezawa, Alhaji Musa Haruna, yayin da yace zasu kaddamar da bincike akan lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel