Malamin addinin Islama ya bukaci gwamnati ta dauki mataki kan kafafen sada zumunta

Malamin addinin Islama ya bukaci gwamnati ta dauki mataki kan kafafen sada zumunta

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Muhammad Nasir Abdul Almuhiyi ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan kafafen sada zumunta ta hanyar kafa cibiya da za ta rika kulawa da yadda ake amfani da shi.

Shiekh Abdul Almuhiyi wadda shine shugaban gudanar da mulki na kungiyar Jama”atul Izalatul Bidia Waikamatussuna (JIBWIS) na kasa reshen Jos ya yi wannan kirar ne yayin da ya jagoranci wata tawagar 'yan kungiyar zuwa ofishin kungiyar 'yan jarida na kasa (NUJ) reshen jihar Kebbi.

Ya ce idan gwamnati na son tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Najeriya, ya zama dole a sanya idanu a kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar kafa wata hukuma da za ta rika kula da lamarin.

Malamin addinin Islama ya bukaci gwamnati ta dauki mataki kan kafafen sada zumunta

Malamin addinin Islama ya bukaci gwamnati ta dauki mataki kan kafafen sada zumunta
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kannywood: Ban durkusa domin bawa Nabruska hakuri ba - Hadiza Gabon

"Muna kira ga gwamnatin tarayya ta dauki mataki a kan wasu barnar da ake yi a kafafen sada zumunta domin hana yaduwar labarin da babu gaskiya cikinsu," inji shi.

Sheikh Almuhiyi ya ce sun kai ziyara sakatariyar NUJ ne domin kara dangon zumunci tsakaninsu da kuma neman goyon bayan su.

Ya shawarci 'yan jarida su guji wallafa labaran da za su iya janyo tashin hankali da tabarbarewar tsaro a kasa.

"Ku kasance masu bitar labaran ku kuma ku tabbatar da gaskiya kafin ku wallafa," inji shi.

Da farko, Shugaban NUJ na jihar Kebbi, Aliyu Jajirma ya ce ziyarar ta zo a lokacin da ake bukatar ta kuma sun karu sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel