Najeriya ta garkame ofisoshin jakadancinta a kasashe 4 saboda rashin kudi

Najeriya ta garkame ofisoshin jakadancinta a kasashe 4 saboda rashin kudi

Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin kullewa tare da garkame ofisoshin jakadancinta dake wasu manyan kasashen duniya guda hudu sakamakon matsalar karancin kudade da gwamnatin ke fama da ita.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministan kula da harkokin kasashen na Najeriya, Mista Geoffrey Onyeam ne ya bayyana haka a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, inda yace wadannan kasashe sun hada da Srilanka, Serbia, Ukraine da Czech Republic.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Dakarun Soji sun tattara mazauna wani kauye sun canza musu wajen zama

Najeriya ta garkame ofisoshin jakadancinta a kasashe 4 saboda rashin kudi

Najeriya ta garkame ofisoshin jakadancinta a kasashe 4 saboda rashin kudi
Source: UGC

Minista Onyeam ya kara da cewa matsalar kudi ta tilasta ma gwamnati rufe wadannan ofisoshinata, wanda hakan yasa bata iya samun daman kulawa da ayyukan yau da kullum a ofisoshin.

A wani labarin kuma, da yammacin ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidarsa Aisha, tare da sauran tawagarsa suka dawo gida Najeriya bayan kwashe kwanaki 5 a kasar Makkah inda suka gudanar da aikin Umrah.

Makusancin shugaban kasa Buhari, kuma hadiminsa na kafafen sadarwar zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, inda ya daura hotunan Buhari da Aisha yayin da suka dawo Najeriya a cikin jirgin shugaban kasa.

“Shugaba Muhammadu Buhari da uwargidarsa, Aisha, sun dawo gida Najeriya da yammacin nan bayan sun gabatar da aikin ibadar Umarah a birnin Makkah dake kasar Saudiyya.” Inji shi.

Dama dai tun da farkon tafiyar ne kaakakin shugaban kasa Garba Shehu ya sanar da cewa Buhari zai yi wannan tafiya ne bisa gayyatar da mai alfarma Sarkin Saudiyya, Sarki Salman yayi masa zuwa kasar Saudi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel