Ana ibada amma Tinubu ya tafi Umrah ya gyaro miyarsa da Buhari – PDP

Ana ibada amma Tinubu ya tafi Umrah ya gyaro miyarsa da Buhari – PDP

Mun ji cewa jam’iyyar PDP ta soki babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, tana mai zarginsa da fitowa yana fadin wasu kalamai da ba su dace ba a game da jam’iyyar hamayyar.

PDP tace Bola Tinubu ya dura kan ta ne domin samun karin shiga a siyasa ba komai ba. Kakakin babbar jam’iyyar adawar na kasa watau Mista Kola Ologbondiyan, ya bayana wannan a wani jawabi da yayi.

Jam’iyyar take cewa ganin yadda Tinubu ya tashi ta-ka-nas har zuwa kasa mai tsaki a cikin Watan azumi domin kurum ya gana da shugaba Buhari ya kuma caccaki PDP ya nuna cewa APC ba ta da inda ta sa gaba.

“Abin kunya ne ace a lokacin da ake kokarin yi wa Najeriya addu’a Ibada a kasa mai tsaki, amma Bola Tinubu ya lula har Makkah, babu abin da ya kai sa illa ya cigaba da buga bakar siyasarsa da kuma zagin jama’a domin ya burge Buhari”

KU KARANTA: Wasu Matasan Arewa sun ce Tinubu ba zai gaji Buhari ba

Ana ibada amma Tinubu ya tafi Umrah ya gyaro miyarsa da Buhari – PDP

PDP ta caccaki ziyarar Bola Tinubu zuwa Umrah wajen Buhari
Source: UGC

“PDP ta lura cewa babu abin da zai kai Asiwaju Tinubu kasar Saudi yana fadan irin kalaman da ya furta na yabon gwamnatin Buhari da ta gaza sai munafunci..

...“Tinubu yayi wannan ne don gujewa barazanar da wasu ke yi na tona asirin sa a fadar shugaban kasa”

Mai magana da yawun jam’iyyar yake cewa:

“Wannan dai shi ne Asiwaju Tinubu, da ya fito cikin Watan Junairu yana sukar gwamnatin Buhari da rashin sanin aiki da kama-karya da kuma tafka badakala a harkar tallafin man fetur…

PDP tayi mamakin ganin yadda aka ji Bola Tinubu yana fitowa yana wani bayani na dabam a yau bayan a wancan lokaci yayi kira ga jama’a su yi tunani kafin zaben shugabannin kasar

A wancan lokaci Tinubu ya koka da yadda dukiyar kasar ta dankare wajen wasu tsiraru wanda hakan ya kawo rashin aikin yi da abubuwan more rayuwa da kuma karancin abinci da talauci.

Wannan ya sa PDP ta caccaki Jagoran na APC ta kuma ce babu abin da zai hana Atiku samun nasara a kan Buhari a zaben na 2019. A karshe PDP ta nemi Tinubu ya shiga taitayinsa inda tace har na-cikin APC sun fara gane shirinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel