Tsaffin hadiman minista sun maka shi a kotu saboda kin biyansu albashi

Tsaffin hadiman minista sun maka shi a kotu saboda kin biyansu albashi

Tsaffin hadiman ministan sadarwa, Alhaji Adebayo Shittu sunyi kararsa a kotu bisa ikirarin cewa ya ki biyansu albashinsu da allawus da ya kai kimanin Naira Miliyan 21.

Hadiman biyu, Razaq Olubodun da Victor Oluwadamilare sun shigar da kararrakinsu ne ta hannun lauyansu mai suna Adewale Lawal inda suke rokon kotu ta umurci ministan ya biya su alabshinsu da hakkokinsu da ya ki biya yayinda suke masa aiki.

A karar da ya shigar a kotun ma'aikata na kasa mai lamba NICN/Abj/132/2019, Olubodun yana neman kotun ta tilastawa ministan biyan shi albashinsa da allawus dinsa na watanni 24 da ua kai N9.8m yayin da Oluwadamilare ya na neman ministan ya biya shi N11.7m a matsayin albashi da allawus dinsa na watanni 28.

Tsaffin hadiman ministan sun maka shi a kotu saboda kin biyansu albashi

Tsaffin hadiman ministan sun maka shi a kotu saboda kin biyansu albashi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Rudani: Kwamandan soji ya kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari a Maiduguri

Hadiman biyu suna neman kotu ta ayyana rashin biyansu albashi da allawus dinsu a matsayin laifi da ya sabawa kudin tsarin mulki tare da tilastawa ministan ya biya su hakokinsu kamar yadda doka ya tanada.

Har ila yau, hadiman biyu ne neman ministan ya biya kowannensu N50m a matsayin kudin da za su biya lauyoyin da suka dauka.

Olubodun ya ce N1m kaccal ministan ya biya shi a tun da ya dauke shi aiki yayin da Oluwadamilare ya ce N2.3m kaccal aka biya shi bayan watanni 28 da ya yi yana yiwa ministan hidima a matsayin hadiminsa na fanin kafafen yada labarai.

Hadiman sun ce wata takarda da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya a ranar 27 ga watan Yulin 1999 ta bayyana cewa albashin hadimi da babban hadimi na minista daidai ya ke da na ma'aikacin gwamnati a mataki na 12 da 16.

Sunyi ikirarin cewa ministan yana yi musu barazana da nuna isa da fin karfi a duk lokacin da suka nemi ya biya su hakokinsu kuma sun sha bakar wahala sakamakon rashin samun hakokinsu daga hannun ministan.

Kotu ta tsayar da ranar 20 ga watan Mayu domin fara sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel