Yaki da ta’addanci: Dakarun Soji sun tattara mazauna wani kauye sun canza musu wajen zama

Yaki da ta’addanci: Dakarun Soji sun tattara mazauna wani kauye sun canza musu wajen zama

Hukumar Sojin Najeriya ta kaddamar da aikin kwashe ilahirin jama’an kauyen Sabongari dake cikin karamar hukumar Damboa ta jahar Borno inda take mayar dasu sansanin yan gudun hijira dake Damboa sakamakon hare haren yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamandan yaki da Boko Haram, Manjo Janar Benson Akinruloyu ne ya sanar da haka ga manema labaru a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, sai dai yaki ya fayyace ko aikin nada alaka da ayyuna Boko Haram.

KU KARANTA: An cigaba da yakin baka tsakanin Atiku Abubakar da yar gidan Buhari

Daga safiyar Talata zuwa yamma Sojoji sun kwashe mutanen kauyen da dama, inda suka debesu a cikin manyan roka roka na Sojoji akalla guda ashirin zuwa sansanin yan gudun hijira dake Damboa.

Idan za’a tuna, ko a farkon watan Afrilun data gabata sai da Sojoji suka kwashe kafatanin al’ummar kauyen Jakana da bai wuce nisan kilomita 20 zuwa birnin Maiduguri ba, inda suka canza musu matsuguni da nufin samun sararin yaki da yan ta’adda.

A wani labarin kuma wasu gungun masu garkuwa da mutane sun kai hari gidan wani jami’in gwamnatin karamar hukumar Toto ta jahar Nassarawa, Mohamamd Shuaibu inda suka bindigeshi har lahira sa’annan suka yi awon gaba da matarsa.

Wani mazaunin unguwar da abin ya faru, Abdullahi Ahmed ya bayyana cewa a makon data gabata ne yan bindigan su biyar dauke da bindigu suka kutsa kai cikin gidan Shuaibu dake unguwan Bai inda suka kashe shi, suka yi garkuwa da matarsa Zainab Salihu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel