Malaman jami’a sun samu tagomashin N25,000,000,000 daga wajen Buhari

Malaman jami’a sun samu tagomashin N25,000,000,000 daga wajen Buhari

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ta amince da biyan Malaman jami’o’in Najeriya hakkokinsu na alawus alawus da suka kai naira biliyan ashirin da biyar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wadannan kudi na daga cikin sharuddan janye yajin aiki da Malaman suka gindaya ma gwamnatin tarayya a yayin da suka kulla yarjejeniya game da kin sake shiga yajin aikin.

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe jami’in gwamnati, sun yi garkuwa da matarsa

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya sanar da haka a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, inda yace baya ga naira biliyan 25, gwamnatin ta rarraba ma jami’o’in Najeriya naira biliyan ashirin a shekarar data gabata.

A cewar ministan, dukkanin jami’o’in gwamnati sun ci moriyar wannan kudi naira biliyan 20, kuma yace gwamnati zata cigaba da kokarin cika duk yarjejeniyar data dauka da ASUU, duk da cewa ta tarar da bashin naira tiriliyan 1.3 da ASUU ke bin gwamnatn baya.

“Sai dai har yanzu akwai kimanin naira biliyan 200 da gwamnati ta umarci babban bankin Najeriya ta baiwa jami’o’in Najeriya tun a shekarar 2013, amma har yanzu kudin basu kare sakamakon rashin cika kaidojin samun kudin.

“Zuwa yanzu dai dukkanin jami’o’in gwamnati guda 73 dake Najeriya sun samu kasonsu daga cikin kashi hamsin da na biliyan 200, yayin da jami’o’I 56 ne kacal suka cika sharadin samun kaso na biyu,wanda ya basu damar yagan rabonsu daga cikin kashi 40 na biliyan 200, amma fa har yanzu babu jami’ar data cika sharadin samun kaso na uku daga cikin kashi goman karshe.” Inji shi.

Daga krshe Ministan yace sun kashe naira tiriliyan 1.38 a sha’anin ilimi a Najeriya ta hanyar tallafi ga NEED, TETFund, hukumar ilimi ta bai daya UBEC, inda yace manyan ayyuka aka gudanar da wadannan makudan kudade.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel