2019: Yaƙin neman kujerar Majalisar Dattawa ya ƙara ƙamari

2019: Yaƙin neman kujerar Majalisar Dattawa ya ƙara ƙamari

Labari ya zo mana cewa fafatukar da ake yi wajen neman shugabancin majalisar dattawan Najeriya ya kara karfi. Yanzu haka masu harin wannan kujera su ne; Ahmad Lawan, Danjuma Goje da Ali Ndume.

Yanzu haka bangarorin wadannan ‘yan siyasa sun bazama da lissafin yawan Magoya bayan da su ke da shi a majalisar tarayyar. Wadannan Sanatoci da ke neman kujerar shugaban majalisa sun dage da samun karin goyon baya.

Sanata Ahmad Lawan ne jam’iyyar APC mai mulki yana bin ‘yan majalisan tarayyar ne dai-daya domin jawo ra’ayin su. Shi kuma Sanata Danjuma Goje yana kokarin samun dunkulen goyon-bayan Sanatocin kasar ne a zaben.

KU KARANTA: Gwamnan PDP yana goyo bayan 'Dan APC a zaben Majalisa

2019: Yaƙin neman kujerar Majalisar Dattawa ya ƙara ƙamari

APC ta tsaida ‘Dan majalisar Yobe Ahmad Lawan ya gaji Saraki
Source: Twitter

Wanda yake yi wa Danjuma Goje wannan aiki a cikin Sanatocin PDP shi ne tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia watau Sanata Enyinnaya Abaribe. Yanzu dai ‘yan takarar na kidiyar Sanatocin da za su yi masu mubaya’a.

A wani bangaren kuma, Sanata Ali Ndume yana yakin neman zaben na sa ne a boye, kamar yadda wata Majiya ta bayyana. Ndume ya ki janye takararsa duk da cewa jam’iyyar APC ta nuna fifiko a kan Sanatan Yobe Ahmad Lawan.

Har yanzu dai babu wanda zai iya cewa ga inda Sanatocin su ka sa gaba, amma ‘yan majalisar adawa sun yi wani zama kwanan nan a gidan Enyinnaya Abaribe domin shirya yadda zaben shugabannin majalisar zai kasance..

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel