An maka Mukaddashin CJN gaban kuliya da laifin karyar shekaru

An maka Mukaddashin CJN gaban kuliya da laifin karyar shekaru

Wani Bawan Allah ‘Dan kasuwa mai suna Tochi Michael ya kai karar mukaddashin Alkalin Alkalan Najeriya, Tanko Mohammed a gaban kotu da zargin yin karya a game da shekarun haihuwarsa.

Kamar yadda labari ya zo mana, Tochi Michael mai shekara 46 ya shigar da karar babban Alkalin kasar na rikon-kwarya ne a gaban kotun tarayya da ke Abuja inda yace CJN din yayi karya a game da shekarun haihuwarsa da gan-gan.

Michael ya fadawa kotu cewa Mai shari’a CJN ya rage shekarun haihuwarsa daga 1950 zuwa 1953. Mai tuhumar babban Alkalin yake cewa an haifi Tanko Mohammed ne a Ranar Disamba 31 ga Watan Afrilun 1950 ba a karshen shekarar 1953 ba.

KU KARANTA: Za a tattara kudin da ke cikin asusun tsohon CJN Onnoghen

An maka Mukaddashin CJN gaban kuliya da laifin karyar shekaru

Ana tuhumar sabon Alkalin Alkalan kasa da laifi a Kotu
Source: Facebook

Wannan ‘dan kasuwa ya bayyanawa kotu cewa Alkali Tanko Mohammed ya zaftare shekaru uku daga cikin shekaran na sa inda yake ikirarin cewa an haife sa a Ranar 31 ga Watan Disamban 1953 a maimakon shekarar sa ta ainihi 1950.

Mai korafin yace takardun babban Alkalin na jarrabawar WAEC sun nuna cewa yayi karya wajen bayyana shekarunsa don haka ya nemi kotu ta kama shi da laifin kage. Laifin kage da ake zargin Tanko da shi, ya sabawa kundin da dokar kasa.

Babban Lauyan da ke kare Alkali Tanko Mohammed watau Sam Ologunorisa ya nemi ayi watsi da wannan kara. Sai dai Alkalin Kotu, Mai shari’a Danlami Senchi ya dage sauraron karar zuwa Ranar Juma’ar nan domin shirin yake hukunci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel