Rashin tsaro: An yi garkuwa da 'yan Najeriya 27 cikin kwanaki 2 a jihohi hudu

Rashin tsaro: An yi garkuwa da 'yan Najeriya 27 cikin kwanaki 2 a jihohi hudu

A yayin da ake ci gaba da fuskantar munanan kalubalai na rashin tsaro musamman a yankunan Arewa, kimanin 'yan Najeriya 27 sun afka tarkon masu ta'addancin garkuwa da mutane a wasu jihohi hudu na kasar nan cikin kwanaki biyu kacal da suka gabata.

Ta'addancin garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa ya zamto ruwan dare da ya yiwa kasar nan dabaibayin da har ila yau ta kasa warware shi. Kazalika ta'addancin 'yan baranda da kuma mafi munin ta'addanci na kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram sun zamto alakakai a Najeriya.

Rashin tsaro: An yi garkuwa da 'yan Najeriya 27 cikin kwanaki 2 a jihohi hudu

Rashin tsaro: An yi garkuwa da 'yan Najeriya 27 cikin kwanaki 2 a jihohi hudu
Source: Facebook

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, duk da tsayuwar daka da jajircewa ta hukumomi masu ruwa da tsaki, annobar rashin tsaro ta ci gaba da ta'azzara tare da kaiwa wani mummunan mataki na intaha da ta ki ci ta ki cinyewa,

Da yawa daga cikin al'ummar Najeriya na ci gaba da kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakamakon gazawar gwamnatin sa wajen samar da tsaro tare da bayar da kariya na tsare rayuwa da dukiyoyin al'umma.

Majalisar wakilai za ta sanya dokar hukunta masu amfani da Leda a Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, al'ummar Najeriya na ci gaba da kalubalantar gwamnatin shugaban Buhari bisa ga madogara ta shimfidar tanadin sashe na 14 cikin kundin tsarin mulkin kasa da ya shar'antawa shugaban kasa samar da tsaro da kuma inganta jin dadin al'ummar sa.

Cikin wani bincike da manema labarai na jaridar Premium Times suka gudanar ya tabbatar da cewa, a tsakanain ranar Lahadi zuwa Talata, azal ta ta'addancin masu garkuwa da mutane ta afkawa mutane 27 a wasu jihohi hudu na Najeriya da suka hadar da Edo, Ekiti, Osun da kuma Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel