Majalisar wakilai za ta sanya dokar hukunta masu amfani da Leda a Najeriya

Majalisar wakilai za ta sanya dokar hukunta masu amfani da Leda a Najeriya

Majalisar wakilai ta Najeriya, ta fara tuntube-tuntuben shawarwari akan kudirin shimfida dokar hana duk wani ta'ammali, samar wa, shigowa ko kuma gudanar da harkokin kasuwanci da leda a fadin kasar nan.

Kudirin ya samu karbuwa a zauren majalisa yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata bisa jagorancin mataimakin kakakin majalisa, Yusuf Lassun. Majalisar na neman murza gashi ta tuburewa wajen sanya dokar haramta ta'ammali da leda yayin gudanar da duk wasu harkoki na yau da kullum a kasar nan.

Zauren Majalisar wakilai

Zauren Majalisar wakilai
Source: Depositphotos

Manufar wannan sabon kudiri da ka iya kasancewa doka a kasar nan ya bayu ne domin takaita illololin da ta'ammali da dukkanin dangin leda kai haifar wa a Najeriya musamman a kan koramu, fadamu, tafki, dajuka, da kuma magudanan ruwa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, kudirin da tuni majalisar dattawan Najeriya ta shigar da shi cikin dokar kasa, ya samu gabatar wa a zauren majalisar wakilai da sanadin dan majalisar APC na jihar Borno, Muhammad Monguno.

A yayin da ta'ammali da leda zai zamto babban laifi a Najeriya, majalisar ta fidda shawarwari na neman dukkanin 'yan kasuwa a kan sauya mazubin hajar su daga leda zuwa na takarda ko kuma su fuskanci fushin doka mai tsananin gaske.

KARANTA KUMA: Ya ci a ce Najeriya ta wuce munzalin daukar nauyin kanta kadai - Osinbajo

Majalisar yayin tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro, ta ce akwai yiwuwar dokar haramcin ta'ammali da leda za ta sanya hukunci na cin tara ta Naira dubu dari biyar ko kuma dauri na zaman a gidan kaso har na tsawon watanni uku. A wani lokacin ta ce masu laifi za su iya fuskantar dukkanin hukuncin guda biyu a tare.

Kazalika majalisar yayin ci gaba da tumke damarar tabbatar da wannan lamari, ta ce dokar za ta yi tanadi hukuncin cin tara ta kimanin Naira miliyan biyar ga kowace kungiya da aka kama da sabawa dokar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel