Ganduje zai sauke mukarrabansa ranar Laraba

Ganduje zai sauke mukarrabansa ranar Laraba

-Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shirya tsaf domin sauke dukkanin mukarrabansa daga kan kujerarsu a ranar Laraba.

-Wannan saukar da hadiman zai zo ne ana saura mako daya kafin a rantsar da gwamnan a karo na biyu ranar 29 ga watan Mayu bayan yayi nasarar lashen zaben gwamnan da ya gabata a jihar Kano.

Kimanin mako guda kan a rantsar da zababbun gwamnoni domin shiga wani sabon wa’adin mulki, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano zai sauke mukarrabansa na majalisar zartarwa guda 13.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa gwamnan zai sauke mukarraban nasa ne a ranar Laraba bayan kammala ganawar majalisar zartarwa ta karshe da su.

Ganduje zai sauke mukarrabansa ranar Laraba

Ganduje zai sauke mukarrabansa ranar Laraba
Source: Twitter

KU KARANTA:Yan bindiga sun sace wasu tagwaye a jihar Ekiti

Amma Shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad Na’iya da kuma sakataren gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji ana tunanin wannan abu ba zai shafesu ba.

Jaridar Guardian ta samu bayanin cewa akwai kishin-kishin din wasu daga cikin kwamishinonin da za’a sauke a ranar Laraba zasu sake dawowa bayan an rantsar da gwamnan a karo na biyu saboda suna da uwa a bakin murhu.

Za’a rantsar da gwamna Ganduje a ranar 29 ga watan Mayu, 2019 bayan da ya samu nasarar lashe zaben gwamnan da ya gabata a jihar Kano.

Gwamnan ya riga da ya sanar cewa zai sauke dukkanin hadimansa kafin ranar 29 ga watan Mayu. Ya kuma sake nanatawa cewa duk wadanda zai dauka a matsayin hadimai a wannan karo sai anyi masu gwaji akan muggan kwayoyi kafin a baiwa mutum wani mukami.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel