Ya ci a ce Najeriya ta wuce munzalin daukar nauyin kanta kadai - Osinbajo

Ya ci a ce Najeriya ta wuce munzalin daukar nauyin kanta kadai - Osinbajo

A yayin da tuni wasu kasashen Duniya da dama suka zamto abin da ake cewa wutsiyar Rakumi ta yi nesa da kasa a fagen taka mataki na ci gaba, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce hakan take ga kasar Najeriya yayin da ta kawo karfi.

Ya ci a ce Najeriya ta wuce munzalin daukar nauyin kanta kadai - Osinbajo

Ya ci a ce Najeriya ta wuce munzalin daukar nauyin kanta kadai - Osinbajo
Source: Facebook

Mataimakin shugaban kasa a ranar Talata ya yi bugun da cewa, kasar Najeriya ta kawo karfi da ta wuce munzalin daukar nauyin kanta kadai. Ya ce ya kamata ta yi koyi da sauran kasashen duniya da suka taka mataki na ci gaba.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin wani taron kasuwanci na kwanaki biyu da kasar Amurka ta gudanar a jihar Legas. Mataimakin shugaban kasar ya yi furucin cewa a halin yanzu ya ci a ce Najeriya ta yi koyi na kulla dangatar daukar nauyi da kulla kyakkyawar dangartaka tamkar wasu kasashen dake nahiyyar Turai, Asia, Gabas ta Tsakiya da sauran su.

KARANTA KUMA: Wata Mata ta gurfana a gaban kotu da laifin yiwa kanta tsirara da kuma fitsari a mimbarin Coci

Osinbajo wanda Ministan masana'antu da hannun jari Dakta Okechukwu Enelamah ya wakilta, ya ce Najeriya za ta kara hobbasa wajen kulla kyakkyawar dangartaka da wasu kasashe daban daban a fadin duniya.

Kazalika tsohon kwamishinan shari'a na jihar Legas ya ce, Najeriya za ta kara kaimi wajen kulla dangartakar cude-ni-in-cude-ka da wasu kasashen duniya domin cin moriyar arzikin juna wajen tabbatuwar ci gaba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel