Yanzu-yanzu: Gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga Femi Gbajabiamila

Yanzu-yanzu: Gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga Femi Gbajabiamila

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana goyon bayansa ga shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, a zaben kujerar kakakin majalisar wakilan da zai gudana a watan Yuni.

Umahi, wanda gwamna na karkashin jam'iyyar adawa Peoples Democratic Party (PDP), ya nuna goyon bayansa ga dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yayinda ya kai masa ziyarar ban girma a garin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ranar Talata.

Tare da zababbun yan majalisa 103, wanda ya hada da AbdulMumini Jibrin, Gbajabiamila ya kai wannan ziyara ne domin neman goyon bayan gwamna Umahi.

KU KARANTA: Shugaban kasar Faransa ya gayyaci Buhari zuwa wani muhimmin taro

Gwamnan ya yi kira ga Gbajabiamila da ya tafiya da kowa majalisar wakilai ba tare da nuna banbancin jam'iyyar siyasa ba.

Wannan abu ba zo da mamaki ba saboda gabanin zaben 2019, gwamna Umahi ya umurci akalla mutane 2000 sun yiwa shugaba Muhammadu Buhari laale marhabun yayinda ya zo yakin neman zabe jihar.

Umahi ya bayyanawa manema labarai cewa ya yi hakan ne saboda shugaban kasa ya cancanci girmamawan da ya dace.

Yace: "Wannan gangamin jama'ar da kuka gani, su 2000, ni na turasu saboda na san APC ba tada kowa. Amma kada a gani cewa mutan jihar Ebonyi ba su so shugaban kasa, shi yasa na umurci mutane 2000 su tarbesa.

Ni ba siyasar ra'ayin rikau nike ba, ni siyasr cigaba nikeyi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel