Rudani: Kwamandan soji ya kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari a Maiduguri

Rudani: Kwamandan soji ya kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari a Maiduguri

An samu sabani tsakanin sojoji da 'yan sanda yayin da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ke kaddamar da wasu ayyuka a ranar Talata a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mataimakin shugaban kasar ya kai ziyar Borno ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Gwamna Kashim Shettima mai barin gado tayi.

Ayyukan sun hada da makarantu, cibiyar GSM da gidajen marayu da suka rasa muhallinsu a jihar.

A lokacin da mataimakin shugaban kasa da Kashim Shettima da maitaimakin gwamna, Usman Durkwa ke kaddamar da wata makaranta a kan titin Bukumkutu a Maiduguri, jami'an tsaro da ke gadinsu sunyi rikici a bainar jama'a.

Rudani: Soji sun kaiwa tawagar Osinbajo hari yayin da ya kai ziyara Borno

Rudani: Soji sun kaiwa tawagar Osinbajo hari yayin da ya kai ziyara Borno
Source: Twitter

Rikicin ya barke ne bayan kwamandan Operation Lafiya, Mike Alechenu ya hana tawagar Durkwa su bi tawagar sauran manyan mutane da suka hallarci taron.

Alechenu ya yi amfani da sanda ya fasa gilashin motar jagoran tawagar Durkwa a lokacin da ya yi yunkurin shiga cikin jerin motoccin sauran manyan mutane da suka hallarci taron.

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Ya kuma yi amfani da sanda ya doki direban wata farar Hilux da ke dauke da jami'an tsaro kafin ya bawa sojojin sa umurnin sace tayar duk wata mota da tayi yunkurin motsawa a cikin tawagar Durkwa.

Sojoji sun makala wuka a jikin bindigarsu inda suke jira su aikata umurnin kwamandan su.

Alechennu ya kuma yi barazanar sanyawa wa dan sandan da ke jagorancin tawagar Durkwa ankwa a yayin da ya ke neman yin sulhu.

"Wannan harkar tsaro ne, ba zaka fada min abinda zanyi ba. Zan daure ka in saka maka ankwa idan kayi motsi daga inda ka ke," Alechenu ya gargadi dan sandan.

Daga bisani jami'an 'yan sanda sun rufe hanya don nuna kin amincewarsu kan abinda ya faru.

"Kana kokarin razana mu amma ka tsere ka bar aikinka na yaki da Boko Haram," inji wani dan fusattacen dan sanda.

Wasu jami'an 'yan sandan farin kaya (DSS) ne suka yi sulhu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel