Wata Mata ta gurfana a gaban kotu da laifin yiwa kanta tsirara da kuma fitsari a mimbarin Coci

Wata Mata ta gurfana a gaban kotu da laifin yiwa kanta tsirara da kuma fitsari a mimbarin Coci

Wata 'yar Tireda mai shekaru 39 a duniya, Moji Aderibigbe, ta gurfana gaban wata kotun majistire da ke zaman ta a unguwar Yaba ta jihar Legas bisa aikata laifin yiwa kanta tsirara tare da yin fitsari a kan mimbarin Coci.

Wata Mata ta gurfana a gaban kotu da laifin yiwa kanta tsirara da kuma fitsari a mimbarin Coci

Wata Mata ta gurfana a gaban kotu da laifin yiwa kanta tsirara da kuma fitsari a mimbarin Coci
Source: Depositphotos

Bayan tafka wannan ta'asa a ranar Juma'a, 17 ga watan Mayu, Moji wadda ta kasance mazauniyar unguwar Pedro a jihar Legas, ta gurfana gaban kuliya da zargi na aikata laifin rashin da'a da kuma wulakantar wa ga addini.

Yayin labartawa manema labarai yadda lamarin mai kama da wasan kwaikwayo ya kasance, jami'in dan sanda Sajen Modupe Olaluwoye, ya ce Moji bayan yiwa kanta tsirara haihuwar Uwa, ta kuma tsula fitsari akan mimbarin wani Coci dake kan titin Onabola a unguwar Barika ta Legas.

Bugu da kari, babban limamin Cocin, Fasto Francis Osibowale, ya shaidawa kotun cewa akwai wani sa'ili da dan Moji mai shekaru goma sha biyar a duniya ya rika bardanatar da kayayyakin cocin Fireband Power Ministry.

KARANTA KUMA: Masu akidar Musuluntar da Najeriya ne kadai za su soki Obasanjo - Fani Kayode ya yiwa Sule Lamido raddi

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, laifin da ake zargin Moji da aikatawa, yana cin karo da sashe na 124 da kuma sashe na 168 sakin layi na daya cikin dokokin miyagun laifuka na jihar Legas da ka shimfida a shekarar 2011.

Akwai yiwuwar laifin wulakanta addini zai haddasa wa Moji daurin shekaru biyu, yayin da laifin ta na nuna fitsara da kuma rashin da'a ta tsare mutuncin kai zai janyo ma ta dauri na watanni uku a gidan Dan Kande ko kuma zabi na cin tara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel