Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude wasu muhimman aiyuka (Hotuna)

Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude wasu muhimman aiyuka (Hotuna)

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude wasu muhimman aiyuka da gwamnatin jihat tayi.

Osinbajo ya sauka a filin jirgin sama na garin Maiduguri da misalin karfe 12:00 na ranar Talata. Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, tare da zababben gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umar Zulum, da ragowar hadiman gwamnatin Borno ne suka tarbi Osinabajo a filin jirgin saman.

Daga cikin aiyukan da Osinbajo ya bude akwai ginin wata katafariyar makarantar firamare da aka saka wa sunan shehun Borno, Abubakar Ibn Umar El-Kanemi. Gwamna Shettima ne ya mayar da ginin wurin ya koma makaranta kasancewar sa gidan yari a baya.

Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude wasu muhimman aiyuka (Hotuna)

Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude wasu muhimman aiyuka
Source: Twitter

Osinbajo a jihar Borno
Source: Twitter

Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude wasu muhimman aiyuka (Hotuna)

Osinbajo ya ziyarci jihar Borno domin bude muhimman aiyuka
Source: Twitter

Kafin tashin sa zuwa kasar Ingila domin yin hutun kwanaki 10, shugaban kasa Muhammadu buhari ya ziyarci jihar Borno tare da bude wasu aiyukan da gwamnatin jihar tayi.

DUBA WANNAN: Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya, ya tashi zuwa Abuja (Hotuna da bidiyo)

Aiyukan ta;addanci na mayakan kungiyar Boko Haram ya jawo koma baya da kusan durkushewar harkokin ilimi, musamman a matakin furamarae da sakandire, a jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel