DPR tayi karin haske kan batun karin kudin man fetur

DPR tayi karin haske kan batun karin kudin man fetur

Mr Antai Asuquo, Kwantrola Janar na Sashin Kula da Albarkatun Man Fetur (DPR) na shiyyar Warri, ya ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar yin karin kudin man fetur a halin yanzu.

Asuquo ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin taron bikin 'Ranar duniya da al'adu da cigaban al'umma' da aka gudanar a ofishohin DPR da ke sassan kasar nan.

Kwantrolan ya bukaci 'yan Najeriya su dena damuwa a kan batun karin kudin man fetur inda ya ce yawan damuwan zai iya janyo cikas wurin samar da man fetur din. Ya kara da cewa akwai man fetur wadatacce kuma farashinsa yana nan a N145 kowanne lita.

DPR tayi karin haske kan batun karin kudin man fetur

DPR tayi karin haske kan batun karin kudin man fetur
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

"Akwai wadataccen man fetur, farashin man fetur (PMS) yana nan yadda aka san shi kuma babu wani shirin yin karin farashi.

"Mu dena ajiye man fetur a na tsawon lokaci domin ajiye fetur a gidajen mu yana da matukar hatsari.

"Rayukan mu da dukiyoyin mu suna da muhimmanci saboda haka ya dace muyi amfani da ma'adinan mu ta hanyar da ya dace," inji shi.

Asuquo ya kuma shawarci 'yan Najeriya su rungumi shirin gwamnatin tarayya na amfani da gas na girki (LPG) inda ya ce akwai wadattacen gas din na girki a kasar.

"LPG shine makamashin da duniya za ta rika amfani da shi a gaba. Yafi tsafta kuma muna da wadattace a kasar nan.

"Ina shawartar mutane su bi tsarin gwamnatin tarayya domin hakan zai zama alheri ga kowa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel