Masu akidar Musuluntar da Najeriya ne kadai za su soki Obasanjo - Fani Kayode ya yiwa Sule Lamido raddi

Masu akidar Musuluntar da Najeriya ne kadai za su soki Obasanjo - Fani Kayode ya yiwa Sule Lamido raddi

Tsohon Ministan harkokin sufuri na jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya yi raddi a kan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, biyo bayan caccakar tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da yayi ikirarin cewa ta'addancin Boko Haram manufa ce ta musuluntar da Najeriya.

Obasanjo a ranar Asabar ba ya ga babatu na bayyana bakin cikin sa akan ta'azzarar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram da kuma na makiyaya, ya yi ikirarin cewa "a halin yanzu babu wani batu na rashin ilimi, rashin aiki ko kuma katutu na talauci a tsakanin matasa da yake ci gaba da rura wutar ta'addanci a Najeriya face miyagun ababe dake aukuwa da manufa ta musuluntar da nahiyyar Afirka baki daya".

Femi Fani Kayode

Femi Fani Kayode
Source: UGC

Obasanjo ya ce "wannan kalubalai da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu sun sha gaban duk wani karfi na gwamnati da ba za ta iya magance shi ba a sakamakon hadin gwiwar mayakan Boko Haram da kungiyar ta'adda mafi muni a ban kasa ta ISIS dake cin karen ta babu babbaka a yankin Afirka ta Yamma".

Tsohon gwamnan jihar Jigawa a ranar Lahadin da ta gabata yayin mayar da martani, ya nemi Obasanjo da ya dawo daga rakiyar wannan mummunan furuci tare da shawartar sa kan cewa kada sabanin sa da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da shi sakarai.

Cikin nasa martanin, tsohon Ministan ya ce hidima da kuma gudunmuwa ta samar ci gaba da Obasanjo ya yiwa yankin Arewacin Najeriya musamman ga 'yan kabilar Fulani da tsohon gwamnan jihar Jigawa ya fito daga cikin su, ta yiwa ta sauran shugabannin kasa da suka shude a baya fintinkau.

A cewar tsohon Ministan, dukkanin wadanda ke sabani ko kuma cin karo da furucin Obasanjo, ba bu shakka su na tarayya da kuma sa hannu akan akidar musuluntar da Najeriya ta hanyar ribatuwa da ta'addanci kungiyar Boko Haram.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel