Gwamnatin jihar Jigawa zata kashe kudade masu yawa domin inganta ruwan sha a Dutse

Gwamnatin jihar Jigawa zata kashe kudade masu yawa domin inganta ruwan sha a Dutse

-Gwamnatin Jigawa na niyyar bunkasa samar da ruwan sha a babban birnin jihar na Dutse

-Wannan kuduri ya kasance daya daga cikin manufar gwamnati, kamar yadda shugaban hukumar bayar da ruwan sha a jihar ya fadi.

Shugaban hukumar samar da ruwan sha na jihar Jigawa, Zayyan Rabiu ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa gwamnati ta bayar da N192m domin inganta samar da ruwa a Dutse, babban birnin jihar.

Shugaban wanda ya bayyana wa kamfanin dillacin labarai na Najeriya NAN, yace manufar yin hakan shine samar da wadatattun ruwan sha zuwa kowane gida dake Dutse kamar yadda gwamnati tayi alkawari.

Gwamnatin jihar Jigawa zata kashe kudade masu yawa domin inganta ruwan sha a Dutse

Gwamnatin jihar Jigawa zata kashe kudade masu yawa domin inganta ruwan sha a Dutse
Source: Twitter

KU KARANTA:Wata sabuwa: Gawar jaririya tayi sama ko kasa a wani asibiti dake Ondo

Shugaban ya kara da cewa, shiyyoyin da basu da ruwa za’a sanya masu tareda da sanya su cikin wannan sabon tsari domin ya kasance sun more samun ingantaccen ruwa.

Ya kuma shawarci jama’a da su guji barnar ruwan, har wa yau su taimaka domin kula da kayayyakin aikin gidan ruwa sabbi da za’a sanya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel