Watan Azumi: Gidauniyar Dangote ta fara ciyar da 'yan gudun hijira a jihar Borno

Watan Azumi: Gidauniyar Dangote ta fara ciyar da 'yan gudun hijira a jihar Borno

Taimako na saukaka radadin halin kakanikayi da 'yan gudun hijira a jihar Borno ke fuskanta ya sauka yayin da gidauniyar nan ta Aliko Dangote ta shimfida hannu ta na jin kai wajen kaddamar da shirin ciyarwa a wannan babban wata na Azumi.

Gidauniyar Dangote a ranar Litinin da ta gabata, ta kaddamar da shirin jin kin da ta saba a kowace shekara na daura damarar ciyar da dubunnan al'umma dake sansanan 'yan gudun hijira a jihar Borno.

Aliko Dangote

Aliko Dangote
Source: UGC

A yayin da akwai kimanin mutane miliyan biyu a sansanan 'yan gudun hijira da ke jihar Borno kamar yadda rahotanni suka bayyana, gidauniyar Dangote a ranar Litinin da ta gabata ta kaddamar shirin malalar da miliyoyin dukiya wajen ciyar da al'umma a sansanai daban daban dake yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya.

Mataimakin gwamnan jihar Borno, Usman Mamman Durkwa, ya halarci bikin kaddamar da shirin yayin da wakilin gidauniyar Dangote, Musa Bala, ya gabatar da kayayyakin abinci masu tarin yawa ga 'yan gudun hijira a kananan hukumomin Konduga da kuma Bama.

KARANTA KUMA: Kotu ta tabbatar da nasarar dan majalisar jihar Kano

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a halin yanzu akwai kayayyakin abinci da suka hadar da Shinkafa, Taliya, Sukari, Gishiri, garin Tuwo, Alkama, Masara da kuma Gero na kimanin Naira Miliyan dari biyu da suka isa jihar Borno domin ciyar da mabukata a sansanan 'yan gudun hijira.

Domin bayar da tallafin jin kai da saukaka radadi na halin kunci, ko shakka babu gidauniyar Dangote da sanadin mamallakin ta, Aliko Dangote, ta batar da kimanin Naira Biliyan Bakwai cikin tsawon shekaru bakwai da suka gabata wajen bayar da tallafi ga al'umma a sansanan 'yan gudun hijira dake fadin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel