Matsalar tsaro ce babbar kalubalen gwamnatin shugaba Buhari - Malamin Addinin Musulunci

Matsalar tsaro ce babbar kalubalen gwamnatin shugaba Buhari - Malamin Addinin Musulunci

- Wani masani a fannin addinin Islama ya bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari matsala daya ta ke da shi, matsalar kuma ita ce fannin tsaro

- Ya ce babu wani rikici da zai kai awa 38 a kasar nan baa tare da an shawo kanshi ba, sai dai idan akwai sa hannun manya a cikin shi

Farfesa Taofeek Abdul-Azeez, masani ne a fannin addinin Musulunci, ya bayyana cewa gwamnati shugaban kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda mutane da dama suke fama da matsalar Boko Haram a yankin arewa maso gabas, ita ma matsalar na damunta.

Farfesa Abdul-Azeez, wanda shine babban limanin Masallacin jami'iar Abuja, ya ce Boko Haram na da burin kafa kasar ta daban a cikin Najeriya, ya kara da cewa abinda mutanen da suka assasata su ka su suyi shine su dinga bai wa gwamnati umarni akan abubuwan da suke so.

Matsalar tsaro ce babbar kalubalen gwamnatin shugaba Buhari - Malamin Addinin Musulunci

Matsalar tsaro ce babbar kalubalen gwamnatin shugaba Buhari - Malamin Addinin Musulunci
Source: Twitter

Ya ce, hare-haren wanda yanzu ya canza salo ya koma rikicin makiyaya, da kuma garkuwa da mutane, an haifar da sune domin a bata sunan gwamnatin shugaba Buhari.

Ya yi jawabin na shi a krshen makon nan da ya gabata a Abeokuta a lokacin da yake gabatar da Tafsirin watan Ramadana a wurin wani taro na kungiyar 'yan jarida ta Najeriya.

KU KARANTA: Bikin rantsar da shugaban kasa: Zamu tabbatar da tsaro ga shugabannin da za su zo ta ya murna - Fadar Shugaban Kasa

Malamin wanda ya bayyana ta'addanci a matsayin sana'a ga matasan kasar, ya bayyana cewa "babu wani rikici ko tashin hankali da zai wuce awa 38 a kasar nan ba tare da an kawo karshen shi ba, sai dai idan yana da hadi da wasu manya a kasar nan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel