Bikin rantsar da shugaban kasa: Zamu tabbatar da tsaro ga shugabannin da za su zo ta ya murna - Fadar Shugaban Kasa

Bikin rantsar da shugaban kasa: Zamu tabbatar da tsaro ga shugabannin da za su zo ta ya murna - Fadar Shugaban Kasa

- A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Sanadiyyar rashin isashen tsaro yasa fadar shugaban kasa ta fito ta na tabbatarwa da shugabannin duniya cewa za ta bai wa duk wani shugaban kasa da ya zo domin taya murna tsaro mai karfi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da tabbaci ga shugabannin kasashen duniya, wurin basu tsaro a lokacin da suka zo gurin bikin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar 29 ga watan Mayun nan, da kuma ranar Demokuradiyya ta kasar nan, ranar 12 ga watan Yunin da zamu shiga.

Ministan Labarai da Al'adu, Mista Lai Mohammed, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a gurin wani taro da aka gabatar a Abuja jiya Litinin.

Bikin rantsar da shugaban kasa: Zamu tabbatar da tsaro ga shugabannin da za su zo ta ya murna - Fadar Shugaban Kasa

Bikin rantsar da shugaban kasa: Zamu tabbatar da tsaro ga shugabannin da za su zo ta ya murna - Fadar Shugaban Kasa
Source: Twitter

"Ina mai tabbatar muku da cewa Najeriya za ta bayar da tsaro ga kowanne shugaban kasa da zai zo bikin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Laraba 29 ga watan Mayu, wanda za a gabatar a filin wasa na Eagle Square da ke Abuja, sannan kuma za a ci a sha a fadar shugaban kasa da yammacin ranar."

KU KARANTA: An kashe mutane 16, an sace mutane 7 a wani rikicin matsafa da ya barke a jihar Rivers

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayyana ranar 29 ga watan Mayu, da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin taya murnar wadannan raneku.

Wannan sanarwa ta biyo bayan, rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da za a yi a karshen wannan watan, yayin da kasar ta ke fama da matsanancin matsalar tsaro a kowanne lungu da sako na fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel