An kashe mutane 16, an sace mutane 7 a wani rikicin matsafa da ya barke a jihar Rivers

An kashe mutane 16, an sace mutane 7 a wani rikicin matsafa da ya barke a jihar Rivers

- Wani rikicin 'yan kungiyar asiri da ya barke a jihar Rivers ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 20, yayin da akasace kusan mutane 7 sanadiyyar rikicin

- Bayan haka kuma rikicin ya yi sanadiyyar asarar dukiya mai dinbin yawa, ciki hadda kone fadar wani sarki dake garin da rikicin ya faru

Kimanin mutane 16 ne aka kashe a wani rikici da ya barke tsakanin 'yan kungiyar asiri a kananan hukumomi guda biyu na jihar Rivers ranar Lahadin nan da ta gabata.

An bayyana cewa an kashe mutane 14 a rikincin 'yan kungiyar asirin da ya barke a kauyukan Kono Boue da Gbam Boue da suke karamar hukumar Khana, yayin da aka kashe wasu mutane biyu kuma a kauyukan Ishiodu, Emohua da suke karamar hukumar Emohua.

Bayan haka kuma mun samu rahoton cewa an sace mutane bakwai a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari karamar hukumar Khana, sannan sunyi sanadiyyar asarar dukiya mai dinbin yawa.

An kashe mutane 16, an sace mutane 7 a wani rikicin matsafa da ya barke a jihar Rivers

An kashe mutane 16, an sace mutane 7 a wani rikicin matsafa da ya barke a jihar Rivers
Source: Depositphotos

Sai dai kuma an samu sabani akab yawan mutanen da suka mutu a karamar hukumar Khana, inda wasu suka bayyana cewa mutane 20 ne, wasu kuma suka ce 14 ne, yayin da hukumar 'yan sanda kuma ta bayyana cewa mutane 5 ne suka rasa rayukan su.

Rikicin Khana ya samo asali ne bayan da 'yan kungiyar asiri na Iceland suka je daukar fansar dan kungiyar su da aka kashe.

Sarkin kauyen Kono Boue, Mai Martaba, Mene Taalor Tornwe, ya nuna rashin jin dadin sa da faruwar lamarin.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura

Sarkin, a lokacin da ya ke magana akan lamarin, ya bayyana cewa rikicin ya yi sanadiyyar asarar dukiya mai yawa ciki kuwa hadda kone fadar shi da aka yi, ya bayyana cewa ya karbi umarni daga gurin gwamnan jihar akan ya tabbatar da zaman lafiya a garin sai gashi wasu tsiraru sun zo suna tada hankalin al'umma.

Haka kuma, shugaban cigaban yankin, Prince Christian Borlo-One, ya bayyana cewa sama da mutane 40 ne aka kashe, inda ya kara da cewa a yanke kawunan wasu daga cikinsu inda aka yi garkuwa da mutane biyar.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro na kasar nan akan su yi gaggawar daukar mataki akan wannan lamari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel