Kalaman Obasanjo kan Boko Haram: Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani

Kalaman Obasanjo kan Boko Haram: Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani

Gwamnatin tarayya ta ce kalaman da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kan yakin da gwamnati keyi da Boko Haram da ISWAP na iya janyo rabuwar kai tsakanin mabiya addinai da mabanbanta kabila a Najeriya.

Gwamnatin ta kuma ce kalaman na da matukar muni kuma abin kunye ne a rika samun dattajo kamar tsohon shugaban kasar yana furta irin wannan kalaman.

A sanarwar da ministan yadda labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya fitar ranar Talata a Abuja, ya ce abin takaici ne mutumin da ya yi yaki domin tabbatar da hadin kan Najeriya ya kuma juya yana neman raba kan kasar.

Kalaman Obasanjo kan Boko Haram: Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani

Kalaman Obasanjo kan Boko Haram: Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani
Source: Twitter

Ya ce Boko Haram da ISWAP kungiyoyi ne na ta'addanci kuma ba su la'akari da addini ko kabilanci yayin kai hare-haren su.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya sake yiwa Buhari kaca-kaca kan batun tsaro

Mohammed ya ce, "Tun lokacin da rikicin Boko Haram ya kunno kai a karkashin mulkin Obasanjo kuma ya yi tsanani a 2009, 'yan ta'addan sun fi kashe musulmi tare da lalata masallatai fiye da mabiya wasu addinin kuma ba a san su da nuna banbanci wurin kisa ko kai hari ba.

"Saboda haka babu hikima wani ya ce Boko Haram da ISWAP suna kokarin 'musuluntar' da Najeriya ne ko Afirka ta Yamma."

Ya kuma Buhari ya riga ya nemi taimakon kasashen ketare wurin yaku da Boko Haram tun kafin Obasanjo ya bayar da shawarar.

A cewarsa, "Jim kadan bayan darewa kan karagar mulki a 2015, Shugaba Buhari ya tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya - Kamaru, Chadi, Nijar, Jamhuriyar Benin - domin hadin gwiwa da su wurin magance 'yan ta'addan."

Hakan yasa aka samu gagarumin nasarar samun galaba a kan kungiyar 'yan ta'addan tare da kwato dukkan garuruwan da suka mamaye a baya.

Ministan ya shawarci tsohon shugaban kasar kada ya bari gabar da ke tsakaninsa da Shugaban kasa ta sha karfin kaunar da ya ke yiwa Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel