Yanzu Yanzu: Buhari ya dage ziyarar kwana 1 da zai kai Imo

Yanzu Yanzu: Buhari ya dage ziyarar kwana 1 da zai kai Imo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soke ziyarar aiki na kwana daya da zai kai jihar Imo a ranar Talata, 20 ga watan Mayu.

Ana sanya ran Buhari zai je jihar Imo don kaddara da wasu ayyuka, ciki harda wani gunkin sa, wanda gwamnatin jihar Imo ta kera. Tuni dai tawagar hadimai da manema labarai suka isa Owerri domin jiran zuwansa.

A cewar wani jawabi, dauke da sa hannun sakataren labaran gwamnanjihar, Sam Onwuemeodo, ya bayyana cewa an dage ziyarar domin Shugaban kasar bai riga ya dawo daga kasar Saudiyya ba inda yake aikin Umurah a wannan shekarar.

Yanzu Yanzu: Buhari ya dage ziyarar kwana 1 da zai kai Imo

Yanzu Yanzu: Buhari ya dage ziyarar kwana 1 da zai kai Imo
Source: UGC

Jawabin yace: “Muna burin sanar da jama’a da mutanen jihar Imo cewa mai girma, Shugaban kasa kuma kwamandan rundunar sojin Najeiya, Muhammadu Buhari GCFR, bai dawo daga kasar Saudiyya ba inda shi da sauran Musulmai daga sassa daban-daban na duniya ke gudanar da Umurah.

KU KARANTA KUMA: Ku sa ran samun ci gaba cikin sauri ta kowani fanni a mulkin Buhari na 2 – Gwamnatin tarayya

“Soboda haka, an dage ziyarar da Shugaban kasar zai kawo jihar Imo don kaddamar da wasu manyan ayyuka da Gwamna Rochas Okorocha yayi a ranar Talata, 21 ga watan Mayu.

“Muna rokon mutanen jihar za su fahimci lamarin,” jawabin ya bayyana cewa za a sanar da sabon ranar ziyarar ga jama’a a lokacin da ya dace.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel