Ku sa ran samun ci gaba cikin sauri ta kowani fanni a mulkin Buhari na 2 – Gwamnatin tarayya

Ku sa ran samun ci gaba cikin sauri ta kowani fanni a mulkin Buhari na 2 – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya a jiya Litinin, 20 ga watan Mayu ta ba yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu zai kawo ci gaba a kasar ta kowani fanni kuma cikin sauri.

Ana shirn sake rantsar da Buhari a karo na biyu cikin mako mai zuwa. Gwamnatin tarayya ta bayar da tabbacin bayan sake duba alkalman tattalin arziki da hukumar kiddidiga ta saki na rubu’in farko na wannan shekarar.

An sake duba bayanin GDP da hukumar kididdiga ta saki ne a taron majalisar zartarwa wanda mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Udoma Udoma, yace lambobin GDP ya nuna ci gaba a habbakar tattalin arziki.

Ku sa ran samun ci gaba cikin sauri ta kowani fanni a mulkin Buhari na 2 – Gwamnatin tarayya

Ku sa ran samun ci gaba cikin sauri ta kowani fanni a mulkin Buhari na 2 – Gwamnatin tarayya
Source: Facebook

Yace majalisar ta lura cewa akwai ci gaba a sauran bangarorin tattalin arziki kamar su farashin kayayyaki, wanda aka samu hauhawa a lokacin zabe, amma a yanzu sun daidaita.

KU KARANTA KUMA: Muna da tabbacin nasarar Atiku a kotun zaben Shugaban kasa - PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa sabanin shahararren hasashen nan da ke yawo, bincike da hujjoji da suka billo sun nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yankin kudu manyan mukamai masu maiko a kasar fiye da yanda yayi a arewa.

Takardu da ke kunshe da nade-naden da Shugaban kasa Buhari yayi a gwamnatinsa na farko a 2015 ya nuna cewa akwai daidaito tsakanin yankunan biyu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel