Maganar Amaechi ta fi kwabo, babu yadda Inyamuri zai zama shugaban kasa a 2023 - Sakataren Ohanaeze Ndigbo

Maganar Amaechi ta fi kwabo, babu yadda Inyamuri zai zama shugaban kasa a 2023 - Sakataren Ohanaeze Ndigbo

Sakatare Janar na kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Uche Okwukwu, ya ce al'ummar yankin kudu maso gabashin kasar nan ne suka haka ramin muguntar da ta wuce kaurinsu ta hanyar nunawa jam'iyyar All Progressives Congress kiyayya a zaben 2019.

Okwukwu ya bayyana goyon bayansa ga ministan sufuri, Rotimi Amaechi, kan maganar da yayi cewa yan kabilar Igbo ba zata samu shugabancin Najeriya a 2023 ba.

Ya yi wannan jawabi ne ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, a birnin Fatakwal, jihar Rivers. Ya siffanta jawabin Amaechi gaskiya karara saboda yan kabilar Igbo sun nunawa shugaba Buhari kiyayya a zaben 2019.

KU KARANTA: Milyan N2.5m na karba cikin N30m kudin fansan surukar gwamna Masari - Mai garkuwa da mutane

A cewarsa: "Maganar Amaechi gaskiya ce saboda sun yaudareshi, sun yaudari Ndigbo. Da kun bi abubuwan da ya faru lokacin da wata kungiya ta alanta goyon bayanta ga shugaba Muhammadu Buhari amma suka tsame Amaechi."

"Ko mun so gaskiya, ko mun ki gaskiya, siyasa zahiri ne. Rashin zaben Buhari da mukayi a kasar Igbo, zai hanamu samun bakin magana a takarar shugabancin kasar 2023."

Kwanan nan, Ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa kabilar Igbo ba tada ta cewa a takarar kujeran shugaban kasa a 2019 saboda irin siyasar kiyayya da bangarancin da suka nuna a zaben 2019.

Kan ta kwana, kungiyar kare hakkin kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta mayar masa da martanin cewa shi ba Allah bane saboda haka bai isa ya zantar da abinda zai faru gobe ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel