An kama wani basarake da dan sanda da suka saci transifoma

An kama wani basarake da dan sanda da suka saci transifoma

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Ebonyi ta tabbatar da kama Sarkin Ipene a karamar hukumar Biase na jihar River, Cif Paulinus Ogbor tare da wani dan sanda mai murabus mai suna Onugh da laifin sace transiforma guda uku.

Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Loveth Odah ta shaidawa Punch cewa Dakarun sojojin Najeriya na 13 Brigade ne suka kama mutanen biyu a garin Unwana a karamar hukumar Afikpo ta Arewa a ranar Juma'a a Ebonyi kuma suka mika su ga 'yan sanda domin cigaba da bincike.

An gano cewa na'urorin samar da wutan lantarkin mallakar garuruwan Umuolo, Etana, Ubum, Edu, Ibini, Afono, Urugbam, Ipene da Rgbor ne duk a karamar hukumar Biase na Jihar Rivers.

An kama wani basarake da dan sanda da suka saci transifoma

An kama wani basarake da dan sanda da suka saci transifoma
Source: Twitter

Wadanda ake zargin duk mazauna garin Ipene ne kamar yadda wani jami'in soji ya shaidawa majiyar Legit.ng.

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

An ruwaito cewa sun fadawa sojojin da ke gadin transifoman cewa za su tafi da su zuwa Calabar ne domin mikawa mai su sai daga bisani 'yan sanda suka kama su a Unwana inda suke kokarin sayar da su misalin karfe 11.30 na daren Juma'a.

A halin yanzu an garzaya da su caji ofis na Abakaliki domin amsa tambayoyi.

Wata majiya ta ce sojojin sun bari sun dauki na'urorin ne saboda sun fada musu cewa su ma'aikatn hukumar rarrba wutar lantarki ne na Enugu.

Majiyar ta ce, "Cif Paulinus na garin Ipene ya zo ya ce yana son gani na amma na fadawa yara na cewa bana bukatar ganinsa domin na san matsalar su.

"Ya ce za a kawo hari a garin sai na ce masa zanyi bincike a kai. Sannan ya ce min na'urorin suna karkashin kulawarsa ne kuma dan kwangilar yana son a kai masa.

"Na bar shi ya dauki na'urorin tunda ya ce suna karkashin kulawarsa ne kuma ya ce dan kwangilar yana da takardun shaidan mallaka kuma idan EEDC sun sani babu wata matsala sai na bar su suka tafi.

"Daga bisani sai na samu labari cewa yan sanda sun kama su a Unwana. Daga baya sai wani ya ce sun tafi su sayar da transiforman ne wanda mallakan garuruwa 10 ne a karamar hukumar Biase a jihar Cross River."

Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta ce an tafi da wanda ake zargin zuwa hedkwatan 'yan sanda na Zone 6 a Calabar domin cigaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel