'Yan bindiga sun sace wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura

'Yan bindiga sun sace wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura

- Wasu 'yaan bindiga sun yi awon gaba da wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura na kasa guda biyu a lokacin da suke kan babbar hanyar Akure zuwa Ilesa

- Hukumar 'yan sanda ta kasa daita ce yanzu haka ta baza jami'an ta domin ceto rayuwar mutanen da kuma kamo barayin a duk inda suke

A jiya Litinin ne 20 ga watan Mayu, 2019, wasu barayi mutanen suka sace wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura na kasa (FRSC) a jihar Osun, a kusa da yankin Erin-Ijesa dake kan babbar hanyar Akure zuwa Ilesa.

A rahoton da muka samu ya bayyana mutanen da aka sace din da Abioye da kuma Bayewuni, an sace su a daidai lokacin da suke kan babbar hanyar Akure zuwa Ilesa, inda suka ga cewa an rufe hanyar sannan 'yan bindigar suka far wa motocin su suka kama su ta karfin tsiya suka wuce da su.

'Yan bindiga sun sace wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura

'Yan bindiga sun sace wasu manyan jami'an hukumar kiyaye hadura
Source: Twitter

A lokacin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Osun, Folasade Odoro, ya ce yanzu haka hukumar ta tura jami'an ta domin kamo 'yan bindigar, inda ya tabbatar da cewa za su yi iya bakin kokarin su wurin ganin sun ceto rayuwar mutanen.

KU KARANTA: An yanka ta tashi: Mutanen da aka kashe aka kone a Kaduna 'yan sanda ne ba masu satar mutane ba

Matsalar ta'addanci dai sai faman karuwa take a Najeriya, musamman ma matsala irin ta satar mutane, wacce yanzu ta zama tamkar sana'a a jihohi da yawa ga matasan kasar nan.

A jiya ne muka kawo muku rahoton yadda wasu fusatattun matasa suka kashe wasu mutane suka kuma sanyawa motarsu wuta, yayin da suke zargin cewa barayin mutane ne suke shirin satar wani mutumi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel