Ba sani ba sabo: Hukumar EFCC na binciken Okorocha da wasu manya a kasar nan

Ba sani ba sabo: Hukumar EFCC na binciken Okorocha da wasu manya a kasar nan

A kokarin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ke yi wurin ganin ta kawo karshen matsalar cin hanci da rashawa a kasar nan, yanzu haka dai hukumar ta sanyo gwamnan jihar Imo mai barin gado, Rochas Okorocha, da wasu manya a kasar nan domin binciken su akan wasu muhimman abubuwa

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasa, Ibrahim Magu, ya tabbatar da cewa hukumar ta na bincikar gwamnan jihar Imo mai barin garo, Rochas Okorocha, tare da wasu wasu mutane.

Magu ya sanar da hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a London jiya Litinin. Yaje kasar Birtaniya dinne domin ya hadu da turawan da suke taimakawa Najeriya akan lamarin fitar da kudade ba bisa ka'ida ba.

Shugaban hukumar ya ce gwamnan jihar ta Imo Rochas Okorocha yana daya daga cikin mutanen da hukumar ta ke bincike.

Ba sani ba sabo: Hukumar EFCC na binciken Okorocha da wasu manya a kasar nan

Ba sani ba sabo: Hukumar EFCC na binciken Okorocha da wasu manya a kasar nan
Source: Facebook

Da aka tambaye shi akan halin da ake ciki wurin binciken, Magu ya ce yanzu hukumar ba za ta bayyana komai ba har sai ta samu kwararan hujjujo akan binciken.

Hakazalika shi ma gwamnan jihar Imo da manema labarai suka tuntube shi jiya Litinin, bai bayar da wani bayani ba.

Okorocha ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta na bincikar shi, inda ya kara da cewa yanzu haka hukumar ta rufe duk wasu hanyoyi na shige da ficen kudi a jihar.

KU KARANTA: Duk budurwar da ta rasa mijin aure ta zo zan samo mata - Mustapha Soron Dinki

Gwamnan ya yi magana da manema labaran ne bayan ya mika wasu asibitoci a hannun wasu kungiyoyin sa kai, a fadarsa dake jihar.

Okorocha zai kammala shugabantar jihar ta Imo a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayu, 2019. Ya fito takarar Sanata kuma ya samu nasara, sai dai kuma hukumar zabe ta kasa ta hana shi takardar komawa, inda ta bayyana cewa wasu daga cikin jami'an hukumar suna ganin akwai lauje cikin nadi a samun nasarar ta shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel