Muna da tabbacin nasarar Atiku a kotun zaben Shugaban kasa - PDP

Muna da tabbacin nasarar Atiku a kotun zaben Shugaban kasa - PDP

- Shari’a na kara zafi tsakanin jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a kotun zaben Shugaban kasa

- PDP ta nuna yakinin cewa dan takararta na Shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai kwato nasararsa a karshe

- Kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa hakan zai yiwu ne kawai idan har kwatin kotun kolin ba su yi son kai ba a shari’an

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu ya nuna yakinin samun nasara ga Atiku Aubakar a kotun zaben Shugaban kasa, idan har kwamitin kotun ba ta nuna son kai a shari’an ba.

Muna da tabbacin nasarar Atiku a kotun zaben Shugaban kasa - PDP

Muna da tabbacin nasarar Atiku a kotun zaben Shugaban kasa - PDP
Source: UGC

Jam’iyyar ta PDP ta jadadda cewa Atiku ne ya lashe zabe, sannan maimakon a bashi hakkinsa, fadar Shugaban kasa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) “sun mayar da hankali suna tozarta shugabanninmu da tayar da zarge-zargen karya akan dan takararmu, Alhaji Atiku Abubakar a kokarin su na janye hankalinmu daga karar da ke gaban kotun zabe” jaridar Vanguard ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai, sakataren labaren PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, yayi zargin cewa “...Shugaba Buhari ya gaza a fanni uku da ya kaddamar da kamfen dinsa na 2015 a kai."

KU KARANTA KUMA: An nemi Sultan ya soki sabbin masarautun Kano

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa guda daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sha’anin kafafen sadarwa na zamani, Lauretta Onochie ta mayar da kakkausar martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar game da barazanar da yayi na maka ta gaban kotu saboda zargin cin mutunci da bata masa suna da yace ta yi.

Atiku Abubakar ta hannun lauyansa, Mike Ozekhome ya nemi Lauretta ta janye zargin da tayi na cewa wai hadaddiyar daular larabawa na neman sa ruwa a jallo, inda yace ta nemi afuwansa, kuma ta buga neman afuwan a manyan jaridun Najeriya guda 6, ko kuma ta biyashi naira miliyan 500.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel