An nemi Sultan ya soke sabbin masarautun Kano

An nemi Sultan ya soke sabbin masarautun Kano

- Gamayyar kungiyoyin jama’a da masu ruwa da tsaki a jihar Kano, sun yi kira ga Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad, da ya soke kafa sabbin masarautu a Kano

- Kungiyoyin sun yi zargin cewa an kafa sabbin masarautun ne ba bisa ka’ida ba

- Mutane dai na ganin Ganduje ya kafa sabbin masarautun ne domin ya kaskantar da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Wasu gamayyar kungiyoyin jama’a da masu ruwa da tsaki a jihar Kano, sun yi kira ga Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Abubakar Sa’ad, da ya soki kafa sabbin masarautu a Kano.

Kungiyoyin, a wani jawabi da suka saki a jiya, Litinin, 20 ga watan Mayu ta hannun Abdullahi Baffa Yola, sun yi zargin cewa an kafa sabbin masarautun ne ba bisa ka’ida ba.

An nemi Sultan ya soki sabbin masarautun Kano

An nemi Sultan ya soki sabbin masarautun Kano
Source: Facebook

“Mun damu sosai akan rashin bin tsari na wannan gwamnati mai ci, rushe dadaddiyar al’ada, kin bin umurnin kotu; yayinda mutanen da ke kokarin wanzar da zaman lafiya ke fuskantar duk wani tozarci, barazana da firgitarwa,” cewar jawabin.

KU KARANTA KUMA: AYCF: Tinubu ya hakura da neman takarar 2023 tun da wuri inji wasu ‘Yan Arewa

A ranar 8 ga watan Mayu ne, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa sabbin masarautu hudu dake da sarakunan yanka masu daraja daya da ta sarkin Kano, mutane da dama na kallon hukuncin gwamnan tamkar yunkurin kaskantar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ne.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel