Yan bindiga sun kashe jami’in gwamnati, sun yi garkuwa da matarsa

Yan bindiga sun kashe jami’in gwamnati, sun yi garkuwa da matarsa

Wasu gungun masu garkuwa da mutane sun kai hari gidan wani jami’in gwamnatin karamar hukumar Toto ta jahar Nassarawa, Mohamamd Shuaibu inda suka bindigeshi har lahira sa’annan suka yi awon gaba da matarsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani mazaunin unguwar da abin ya faru, Abdullahi Ahmed ya bayyana cewa a makon data gabata ne yan bindigan su biyar dauke da bindigu suka kutsa kai cikin gidan Shuaibu dake unguwan Bai inda suka kashe shi, suka yi garkuwa da matarsa Zainab Salihu.

KU KARANTA: Yan Shia sun harba nukiliya kasar Makkah yayin da Musulmai ke gudanar da Umarah

Makwabcin ya bayyana cewa daga bisani yan bindigan sun nemi yan uwan matar, inda suka nemi a biyasu naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa kafin su sakota.

Sai dai da fari gungun yan bindiga sun fara yin awon gaba da mutane biyar a kauyen Yelwa na karamar hukumar Toto, mutanen sun hada da Basaru Rukaiya, Aishat Zakari, Chinedu Ide, Reuben Ibram da Vivian Ibrahim, kafin washegari suka kai ma Shuaibu hari.

Da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar Nassarawa,Bolan onge, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai yace rahoton daya samu ya nuna masu garkuwa da mutane guda biyu ne, kuma Yansanda sun dukufa bincike akansu.

Daga karshe kwamishi Longe yayi kira ga jama’a dasu taimaka ma Yansanda da sahihan bayanai da zasu taimaka musu wajen kawo karshen miyagun mutane a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel