AYCF: Tinubu ya hakura da neman takarar 2023 tun da wuri inji wasu ‘Yan Arewa

AYCF: Tinubu ya hakura da neman takarar 2023 tun da wuri inji wasu ‘Yan Arewa

- Kungiyar AYCF tayi magana a kan takarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023

- AYCF tace ka da Tinubu ya bata lokacinsa ya tsaya neman mulkin Najeriya

- Matasan sun ce za su yi kokarin ganin wannan shiri sam bai cin ma ruwa ba

A jiya ne kungiyar nan ta Arewa Youths Consultative Forum (AYCF) ta fito tayi magana a kan shirin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023. Kungiyar tace Tinubu ya daina tunanin zai yi mulkin kasar.

AYCF tayi wannan jawabi ne ta bakin shugabanta watau Yerima Shettima wanda yace yanzu haka kasar Yarbawa ta ke morewa gwamnatin APC. Shettima yake cewa an fifita Kudu maso yamma a kan Arewacin kasar a wannan mulki.

Shettima yake cewa:

“Mutanen Kudu maso Yamma sun yi amfani da dabarun siyasa wajen ganin sun karbe manyan mukamai masu tsoka a gwamnati da kuma ayyukan da ake yi a Najeriya, wannan ya sa yankin Arewa ya zama banza a wannan tafiya…”

KU KARANTA: Yadda aka saki Malamin da aka daure saboda sukar Buhari

Shugaban na AYCF yace:

“A dalilin haka babu wanda zai kawowa Arewa maganar mulki a 2023..”

A jawabin na Shettima ya kara da cewa:

“Bola Tinubu zai bata lokacinsa ne kurum a 2023 don ba zai yiwu yayi mulki ba domin kuwa Najeriya ba kasar kowa ba ce, kuma za mu yi duk wani tanadi na ganin Tinubu bai kai labari ba…”

Duk a jiyan kuma 20 ga Watan Mayu, kungiyar Ohanaze Ndigbo ta fito ta bayyana cewa ka da babban jigon na APC, Bola Tinubu yayi gigin tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel