Yan bindiga sun sace wasu tagwaye a jihar Ekiti

Yan bindiga sun sace wasu tagwaye a jihar Ekiti

-Wasu yan bindiga sunyi awon gaba da mutane uku a jihar Ekiti, biyu daga ciki kuwa tagwaye ne.

-Hukumar yan sandan jihar tace, tana kan aikin ganin cewa an kubuto da wadannan mutane daga hannu wadanda sukayi garkuwa da su.

Wasu yan bindigan da ba’a san ko su waye ba sunyi gaba da mutum uku akan hanyar Aramoko-Efon a jihar Ekiti. Biyu daga cikin wadannan mutane tagwaye ne kamar yadda labara ya zo mana.

Taiwo da Kehinde sune tagwaye da yan bindigan suke sace, yayin da na ukun su shine Mista Ayo Oladele wadanda aka sace a lokuta daban daban.

Yan bindiga sun sace wasu tagwaye a jihar Ekiti

Yan bindiga sun sace wasu tagwaye a jihar Ekiti
Source: UGC

KU KARANTA:Duk budurwar da ta rasa mijin aure ta zo zan samo mata - Mustapha Soron Dinki

Majiya daga bakin iyalan tagwayen tace, wadanda sukayi garkuwa da tagwayen sun kira waya inda suka nemi a basu N6m akan ko wane mutum guda.

Kazalika iyalan Oladele sun sanar da mu cewa yan bindigan sun nemi a basu N10m domin kan su saki mista Ayo. Iyalan wadannan mutane da aka sace sun ce basu da masaniya akan inda aka kai diyansu.

Hanyar Aramoko-Efon ta shahara kwarai da gaske wurin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane, a dalilin hakan nema a shekarar da ta gabata aka aika jami’an soji dajin domin su fatattaki yan ta’addan yankin.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jihar, Mista Caleb Ikechukwu ya tabbatarr da aukuwar wannan lamari, kuma ya bayyana cewa hukumar na kokarin ganin yadda za’a kwato wadannan mutane daga hannun masu garkuwar domin su kasance cikin yanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel