An damke wasu ‘Yan Najeriya da laifin shiga da makamai da ƙwayoyi zuwa Turai

An damke wasu ‘Yan Najeriya da laifin shiga da makamai da ƙwayoyi zuwa Turai

Labari ya iso mana daga wata jairdar Ƙasar waje cewa wasu ‘Yan Najeriya har 3 ne za su yi zaman kaso a Ƙasar Ingila bayan da kotu ta same su da laifin safarar makamai da kuma ƙwayoyi zuwa cikin Turai.

EuroTunnel ta rahoto cewa kotun Woolwich Crown da ke zama a Landan ya kama wasu ‘Yan Najeriya da laifin kitsa ƙulalliya da kuma shiga da mugayen makamai da miyagun ƙwayoyi zuwa Birtaniya.

A hukuncin da wannan kotu ta Landan ta yanke a Ranar Juma’a, 17 ga Watan Mayun 2019, an samu Kennedy Udo mai shekaru 28 da laifin shiga Landan da ƙwayoyi da wasu kaya da aka haramta.

KU KARANTA: Sojoji sun kama masu satar Jama’a a Dajin Taraba da Benuwai

An damke wasu ‘Yan Najeriya da laifin shiga da makamai da ƙwayoyi zuwa Turai

Michael Mgbedike, Kennedy Udo da Emmanuel Okubote.
Source: UGC

Wannan ya sa aka yankewa wannan Saurayi da ya fito daga Najeriya zaman gidan yari na watanni 6. Haka zalika an kuma kama Michael Mgbedike mai shekara 22 da haihuwa da laifin safarar ƙwaya.

Sai kuma wani Matashi mai shekara 23 mai suna Emmanuel Okubote da aka samu da hannu dumu-dumu wajen shiga da manyan makamai cikin Ingila da kuma laifin ƙoƙarin mallakar manyan bindigogi.

Jami’an ‘Yan Sanda ne dai su ka cafke wadannan masu laifi kuma su ka mika su gaban Alkali, wanda ƙarshe aka yanke masu hukunci bayan an same su da hannu wajen safarar ƙwaya da makamai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel