Rikicin APC: Yari yana so yayi amfani da sunan Buhari ya canza hukuncin Kotu – Marafa

Rikicin APC: Yari yana so yayi amfani da sunan Buhari ya canza hukuncin Kotu – Marafa

A daidai lokacin da ake jiran kotun koli ta yanke hukunci a game da rikicin APC a jihar Zamfara ne aka ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi buda-bakin azumi tare da gwamna Abdulaziz Yari.

Sanata Kabiru Marafa ya fito ya koka a game da wannan zama da aka yi tsakanin shugaban kasar da kuma gwamnan na Zamfara, inda yace gwamnan yana kokarin hana kotu tayi aikin ta ne yadda ya dace.

Fitaccen ‘dan majalisar yayi kira ga babban kotun kasar da ta yanke hukunci na adalci, tayi watsi da bilinbituwar da gwamna Abdulaziz Yari yake yi na kokarin nunawa Duniya cewa yana tare da Buhari.

Sanatan yake cewa:

"Gantalin da Yari yake yi, yunkuri ne na nunawa Alkalan Kotun koli da sauran mutanen Najeriya cewa shugaban kasa Buhari yana goyon bayan wannan danyen-aiki da yake yi…"

Sanatan na APC ya kuma kara da cewa:

"Ina tabbatar da cewa Shugaba Buhari ba ya tare da duk wani mugun mutum maras adalci. Shugaban kasa Buhari yana nan duk inda gaskiya ta ke, kuma burinsa ganin an yi wa kowa adalci a APC..."

”Za a fahimci hakan ne a lokacin da shugaban kasar ya fadawa duk wanda ba su gamsu da matakin da APC ta dauka ba, su tafi kotu."

‘Dan majalisar ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Buhari da kan-sa bai jin dadin abubuwan da ke faruwa a jihar Zamfara.

“Bari in fadawa kowa wannan, shugaban kasa bai taba jin dadin abin da ya faru da APC a jihar Zamfara ba, kuma yana tare da jama’ar jihar a kan wannan lamari, masu kokarin amfani da sunan shugaban kasa domin cin ma matsayarsu, makiyan jihar Zamfara ne”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel