Aikin hajjin 2019: Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta fadi jiragen da zasuyi jigilar maniyyatan wannan shekara

Aikin hajjin 2019: Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta fadi jiragen da zasuyi jigilar maniyyatan wannan shekara

-Kamfanonin jiragen sama guda uku ne zasuyi jigilar maniyyata lokacin aikin hajjin 2019, a cewar hukumar aikin hajji ta kasa.

-Wadannan jiragen su ne, Medview, MaxAir da kuma Flynas wanda yake mallakar kasar Saudiya

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta kulla yarjejeniya da kamfanin jiragen sama guda uku domin jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiya a lokacin aikin hajjin 2019.

Fatima Usara wacce ke kula da sashen hulda da jama’a na hukumar ce ta fitar da wannan sanarwa ta hannun manema labarai ranar Litinin a Abuja.

Aikin hajjin 2019: Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta fadi jiragen da zasuyi jigilar maniyyatan wannan shekara

Aikin hajjin 2019: Hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta fadi jiragen da zasuyi jigilar maniyyatan wannan shekara
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Abinda Tinubu ya fada ma Buhari yayin haduwarsu a kasar Makkah

Tace kamfanoni da sukayi yarjejeniya da su sun hada, Max Air Ltd, Medview Airlines Plc da FlyNas wanda yake mallakar kasar Saudiya.

Wannan sanarwa ta samu ne a daidai lokacin da Fatima ke sanya hannu akan takardar yarjejeniyar wacce ta gudana a babban ofishin hukumar dake Abuja.

Tace, “ Jiragen Max Air zasu dauki kashi 51 na maniyyatan wadanda suka fito daga jihohin, Adamawa, Bauchi, Binuwe, Borno, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Nasarawa, Neja, Filato, Taraba da Kogi.

“ Jiragen Medview kuwa kashi 14 na maniyyatan zasu dauka daga jihohin: Akwa Ibom, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Kaduna, Ogun, Ondo, Yobe, Abia, Imo, Anambra, Bayelsa, Rivers da kuma jami’an tsaro.

“ Yayin da Flynas kuma keda kashi 35 na maniyyatan wadanda suka fito daga jihohin: Sokoto, Oyo, Osun, Edo, Kebbi, Lagos, Zamfara da birnin tarayya Abuja.”

Kamar yadda ta fadi, shugaban hukumar Abdullahi Mukhtar ya nemi masu jiragen da suyi aikin da kwarewa domin samun sauki ga maniyyatan yayin da suka kulla niyyar tafiya Saudiya domin sauke farali.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel