Abinda Tinubu ya fada ma Buhari yayin haduwarsu a kasar Makkah

Abinda Tinubu ya fada ma Buhari yayin haduwarsu a kasar Makkah

Tsohon gwamnan jahar Legas, kuma jigo a jam’iyyar APC Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya aike da wani muhimmin sako ga dattawan Najeriya dasu guji furta kalaman da ka iya tayar da hankula a tsakanin al’ummomin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Tinubu ya bayyana haka ne jim kadan bayan kammala zaman buda baki da yayi tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar daya gudana a kasar Makkah.

KU KARANTA: Mutane 2 sun sheka barzahu bayan gamuwa da ajalinsu a cikin ruwan Kano

Abinda Tinubu ya fada ma Buhari yayin haduwarsu a kasar Makkah

Buhari a Makkah
Source: Twitter

Wannan batu na Tinubu tamkar jirwayi ne mai kamar wanka, ko kuma ace hannunka mai sanda ne yake zungurar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ita biyo bayan kalaman da Obasanjo yayi a karshen makon data gabata yana cewa an kirkikiri rikicin Boko Haram da hare haren Fulani ne domin mayar da kowa Musulmi a yankin Afirka ta hanyar Jahadin Musulunci.

Kaakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ne ya bayyana cewa Tinubu yayi kira ga yan Najeriya dasu baiwa gwamnatin Buhari goyon baya tare da hadin kai don ganin daidaita kasar tare da shawo kan kalubalen da take fuskanta.

“Shugaban kasa na aiki tukuru, kuma zai cigaba da aiki tukuru don ganin an tabbatar da zaman lafiya da daidaito a Najeriya, domin dasu ne kadai za’a samu tattalin arziki mai inganci a kasa, don haka ya kamata mu taru mu goya masa baya.” Inji shi.

Daga karshe Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya jinjina ma shugaba Buhari sakamakon amincewa da yayi da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar bikin Dimuradiyyar Najeriya, wanda za’a fara bikin a bana.

Sauran wadanda suka halarci wanann buda baki sun hada da Sarkin Kazaure, Najib Hussaini Adamu, dan uwan Buhari Alhaji Mamman Daura, aminin Buhari kuma surukinsa Sama’ila Isa Funtua, jakadan Najeriya a Saudiyya, Mai sharia Isa Dodo, Wale Tinubu da kamishinan kimiyya da fasaha ta jahar Legas, Hakeem Fahm.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel