Hukumar Hizbah ta damke karuwai 14, ta kwace kwalaben barasa 100

Hukumar Hizbah ta damke karuwai 14, ta kwace kwalaben barasa 100

Hukumar Hisban jihar Jigawa ta damke yan gidan magajiya 14 kuma sun garkame kwalaben barasa 100 a garin Kazaure, hedkwatan karamar hukumar Kazaure.

Hisbah, hukuma ce da aka kafa domin dabbaka shari'ar addinin Musulunci iya gwargwado a jihar Kano da Jigawa.

Kwamdandan hukumar na jihar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu, 2019.

Kana ya ce an kama mazaje bakwai, hakan ya sa jimmilar wadanda aka garkame ya zama 21.

Game da cewarsa, jami'an hukumar sun yi wannan kamu ne a harin da suka kai shahrarren mashayar Gadar Kazaure. Ana tuhumarsu da laifin batanci da lalata a gari.

Yace: "Yan gidan magajiya 14 da mazaje bakwai muka kama. Bayan kammala bincike an gurfanar da su a kotun Kazaure."

A bangare guda, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yace Hukumar Hizba ko ‘Yansandan Shari’a na karkacewa daga turbar da aka dora ta akai kuma tana bukatar ayi mata garambawul.

“Gwamnati ba za ta kara amincewa da irin ayukkan da ba su dace ba da shugabannin Hizbah ke aikatawa” In ji gwamna.

Bayan wannan jawabi da yayi, kwamandan hukumar, Sheik Aminu Ibrahim Daurawa, yayi murabus daga kujeransa matsayin shugaban hukumar.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel