Shugabancin majalisa: Buba ya janye wa Gbajabiamila

Shugabancin majalisa: Buba ya janye wa Gbajabiamila

Mamba a majalisar wakilai daga jihar Adamawa, Honarabul Yusuf Buba, ya sanar da cewar ya janye takarar neman shugabancin majalisar da yake yi tare da bayyana goyon bayan sa ga takarar mamba a majalisar daga jihar Legas, Femi Gbajabiamila.

Buba ya sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja ranar Litinin, ya ce ya yanke shawarar janye wa domin girmaman tsarin jam'iyya APC na tabbatar da daidaito a rabon mukaman gwamnati.

Dan majalisar ya ce ya gamsu da cewar akwai bukatar kowanne bangare na kasa ya samu wakilci a cikin gwamnati, musamman gwamnatin da aka kafa ta a doron dimokradiyya.

Buba, mai wakilatar mazabun Gombi da Hung a jihar Adamawa, ya ce duk da yana da karfin da zai iya lashe zaben kujerar shugaban majalisar, bashi da zabi da ya wuce ya janye domin girmama jam'iyyar sa, APC.

Shugabancin majalisa: Buba ya janye wa Gbajabiamila

Femi Gbajabiamila
Source: UGC

Jam'iyyar APC ta mika kujerar shugabancin majalisar wakilai ga yankin kudu maso yamma tare da bayyana Gbajabiamila a matsayin dan takarar ta.

DUBA WANNAN: Kudin LGAs: Gwamnoni sun bukaci Buhari ya tsawatar wa NFIU a kan sa musu ido

Buba ya bayyana cewar yankuna 6 da kasar nan keda su na da mambobin dake da nagartar zama shugaban majalisar wakilai, tare da bayyana cewar jam'iyya ce ta fito da tsarin rabon mukamai domin samun maslaha.

A watan Maris ne Buba ya bayyana niyyar sa ta yin takarar kujerar majalisar wakilai.

Ya yi kira ga magoya bayan sa dasu fahimci dalilin sa na janye takara tare da neman goyon bayan su wajen hada karfi wuri guda domin kafa shugabancin majalisa mai nagarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel