Mai daki na ta hana ni kusantuwa da ita saboda ƙanƙantar Mazakuta - Fasto ya shaidawa Kotu

Mai daki na ta hana ni kusantuwa da ita saboda ƙanƙantar Mazakuta - Fasto ya shaidawa Kotu

Limamin coci, Fasto Samson Farounbi, ya shaidawa wata kotun al'adu dake zaman ta a birnin Ibadan na jihar Oyo cewa, ƙanƙanuwar mazakuta da ya mallaka ta sanya mai dakin sa ta kauracewa kusantar sa har na wani tsawon lokaci.

Mai daki na ta hana ni kusantuwa da ita saboda ƙanƙantar Mazakuta - Fasto ya shaidawa Kotu

Mai daki na ta hana ni kusantuwa da ita saboda ƙanƙantar Mazakuta - Fasto ya shaidawa Kotu
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Fasto Samson ya shaidawa kotun ta al'adu yayin zaman da ta gudanar a ranar Litinin dangane da koken sa neman sawwake auren da ke tsakanin sa da Uwar gidan sa, Tope Farounbi.

Yayin rokon kotun da ta raba auren su bayan shekaru goma sha tara, Fasto Samson ya nemi adalcin kotun domin samun nutsuwa da kuma kwanciyar hankali a rayuwar sa da ya rasa tsawon lokaci mai girman gaske.

Da yake shaidawa kotun irin halin kunci da ya ke fusanta, Limamin cocin wanda uwargidan sa ta kasance mai sayar da kayan itatuwa, ya ce baya ga haramta masa kusantuwa da ita, ta kan raba dare gabanin dawowa gida a kowace rana.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Imo a ranar Talata

A bisa al'ada ta neman sulhu a tsakanin ma'aurata, Tope ta shaidawa mai gidan ta cewa ƙanƙanuwar mazakuta da ya mallaka ta sanya ba za ta lamunci kusantar sa ba. Sai dai ta yi kokarin nema masa magungunan gargajiya domn samun waraka.

Cikin iko na kotu, jagoran Alkalai Mukaila Balogun tare da sauran alkalai biyu; Wahab Papoola da kuma Alao Ganiyu, sun yanke shawarar raba auren da ke tsakanin Fasto Samson da kuma mai dakin sa Tope a bisa hujja ta rashin cika daya daga cikin manyan shika-shika na zaman aure.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel