Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Imo a ranar Talata

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Imo a ranar Talata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ta mako mai zuwa zai kai ziyarar aiki da wuni guda a jihar Imo domin kaddamar da wani katafaren aikin filin jirgin saman kasa da kasa na Sam Mbakwe da ya lashe biliyoyin dukiya.

Cikin wata sanarwa da sa hannun sakataren sadarwa na fadar gwamnatin jihar Imo, Sam Onmuemeodo, ya ce shugaban kasa Buhari zai kuma kaddamar da sabon ginin zamani na hedikwatar ofishin 'yan sanda da kuma hedikwatar hukumar gidajen yari.

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Imo a ranar Talata

Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Imo a ranar Talata
Source: Twitter

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a karshen makon da ya gabata ya ziyarci jihar Imo, inda ya kaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba da gwamna Rochas Okorocha ya dauki nauyin aiwatar wa.

Ire-iren ayyuka da mataimakin shugaban Najeriya ya kaddamar a jihar Imo sun hadar da sabbin ayyukan gine-gine na saukar baki da kuma asibiti a fadar gwamnatin jihar, manyan titunan Sam Mbwake da kuma na Nnamdi Azikwe.

Gabanin ziyarar mataimakin shugaban kasa a makon da ya shude, akwai manyan Sarakunan gargajiya na Najeriya da suka ziyarci jihar Imo domin kaddamar da wasu muhimman ayyukan ci gaba masu tasiri da inganta jin dadin rayuwar al'umma.

KARANTA KUMA: Shehin Malamin Izala, Mustapha Konduga ya riga mu gidan gaskiya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, manyan Sarakuna da suka ziyarci jihar Imo sun hadar da Sultan na Sakkwato Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, Oba Adeyeye na masarautar Ife, Farfesa Alfred Achebe Sarkin Onitsha, sarkin Calabar Edidem Ekpo Okon da kuma sauran manyan sarakunan gargajiya na kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel